Hotunan manyan coci-coci 8 mafiya kyau a duniya
Wadannan hotuna ne na wasu daga cikin manya-manyan coci-coci mafiya kyau fadin duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Cocin St. Peter's Basilica da ke Vatican City. An fara gina cocin a 18 ga watan Afrilun 1506 aka kuma kammala a 18 ga watan Nuwambar 1626.
Asalin hoton, Getty Images
Cocin Florence Cathedral da ke kasar Italiya. Asalin suna cocin shi ne Cattedrale di Santa Maria del Fiore, kuma an fara ginata a 1296 aka kuma kammala a 1436.
Asalin hoton, Getty Images
Cocin Hagia Sophia da ke kasar Turkiyya kuma an gina ta a shekarar 537.
Asalin hoton, Getty Images
Cocin Liverpool Cathedral da ke Ingila kuma an kammala gina cocin a 1978.
Asalin hoton, Getty Images
Cocin Milan Cathedral da ke Italiya kuma an kammala ginin cocin ne a 1965.
Asalin hoton, Getty Images
Cocin San Petronio Basilica da ke Italiya. An fara ginin cocin ne a 1390, sai aka kammala a 1954.
Asalin hoton, Getty Images
Cocin Seville Cathedral da ke kasar Spain kuma an kammala ginita a 1528.
Asalin hoton, Getty Images
Cocin Ulm Minster da ke kasar Jamus kuma an fara ginin Cocin a 1377 sai aka kammala a 1890.