Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani malamin addinin Kirista kenan ya ke kona turaren wuta a a ranar Lahadi a Cocin Lady of Grace Catholic da ke Mozambique.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wata mace 'yar kabilar Samburu rike da allo a wani tattaki na duniya da ake yi wa Giwaye da dorinar ruwa da zakuna da sauran dabbobin dawa da rayuwarsu ke cikin hatsari a ranar Asabar a birnin Nairobi da ke Kenya.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata yarinya kenan da likita ke taimaka mata wajen koyon tafiya bayan an saka mata kafar roba a Sudan ta Kudu a ranar Jumma'a.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yara na buga kwallon kafa a filin wata makaranta da ke Mozambique a ranar Litinin.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wata matashiya bayan ta bursuna wa kanta dorowar hoda a wani bikin launi na farko a birnin Giza da ke Masar.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mai basirar zane kenan dan kasar Kenya mai suna Bankslave a lokacin da yake kammala zane a bango a birnin Dakar da ke Senegal a lokacin bikin zanen bango da aka yi a kasar a ranar Jumma'a.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sanda da jami'an tsaron fadar shugaban kasa a yayin da suke kokarin tabbatar da tsaro a lokacin da Felix Tshikedi ke isowa filin jirgin Goma da ke kasar Kongo.
Hakkin mallakar hoto Mary Evans Picture Library
Image caption 'Yan wasan Kokawa kenan a birnin Legas da ke Najeriya ya yin da ake gasar Kokawar a gaban dumbin jama'a.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani soja kenan daga cikin sojojin Libya kuma dan gani kashenin shugaban sojojin kasar Khalifa Haftar a yayin da yake nuna bajintar karfinsa wajen fasa bulo a ranar yayensu daga makaratar horon sojoji a Benghazi a ranar Alhamis.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A Sudan, mata ba a barsu a baya ba wajen kiraye-kiraye ga gwamnatin riko ta kasar da ta hambarar da Omar al-Bashir a kwanakin baya da ta mika mulki ga farar hula.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wadannan 'yan matan sun shiga zanga-zangar da ake yi na dawo da mulkin dimokradiyya a kasar.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Diyar shugaban Amurka Ivanka Trump a lokacin da ta kai ziyara ga kananan masu sana'a a Ivory Coast a ranar Laraba a matsayin daya daga cikin ziyara ta kwana hudu da ta kawo wa nahiyar Afirka.

Labaran BBC