An yanke wa iyaye daurin rai da rai kan horar da 'ya'yansu

Bayanan bidiyo,

Daya daga cikin Yaran Turpin na jawabi bayan yanke wa iyayensa hukunci

Wasu ma'aurata a jihar Carlifonia ta Amurka sun samu afuwar 'ya'yansu bayan kotu ta same su da laifin azabtarwa da jefa yaran cikin yunwa shekara da shekaru.

'Ya'yan David da Louise Turpin sun shaida wa Kotu cewa suna matukar kaunar iyayensu duk da cin zarafin da suka sha a hannusu.

A cikin watan Janairun bara aka cafke iyayen lokacin da 'yarsu mai shekara 17 ta tsere daga gidansu da ke Perris.

Iyayen sun amsa laifin da aka tuhume su da shi kan 12 daga cikin 'yaransu 13 a tsawon shekara 9.

Asalin hoton, David-Louise Turpin/Facebook

Bayanan hoto,

Akwai hotunan yaran da dama a shafin Facebook din iyayensu

Iyayen za su shafe tsawon rayuwarsu a kurkuku, sai dai idan an yi musu afuwa a cikin shekaru 25.

Me yaran suka ce?

Ma'aurantan sun fashe da kuka lokacin da suka ji irin bayanan da ke fito wa daga bakin hudu daga cikin yaran na su a lokacin sauraron karar.

''Ina matukar kaunar iyaye na sosai,'' kalaman daya daga cikin yaran kenan.

''Duk da cewa ana ganin yanayin su na tarbiyar damu bai dace ba, na ji dadin irin salon tarbiyatarwar su saboda a yau ina alfahari da mutumin da na zama.''

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

David Turpin ya fashe da kuka lokacin da aka yanke masa hukunci

Shi ma daya cikin yaran ya bayyana irin halin da wannan al'amari ya jefa su.

''Ya ce ba zan iya bayanan irin halin da muka shiga ba lokacin da muke tasowa.''

''Wani lokaci ina mafarkin abubuwan da suka faru, ina hango yadda aka rinka daure 'yan uwa na da dukan da suka sha.

''Abu ne da ya riga ya wuce yanzu lokaci ne na fuskantar zahiri.

''Ina son iyayena kuma na yafe duk abubuwan da suka yi mana.''

Sai dai ba dukkanin yaran ba ne ke da ra'ayi guda kan sassantawa ba.

Wata diyarsu, ta girgiza kai, ta ce: "Iyaye na sun sace mu kuruciyata, amma yanzu lokaci ne na fanshewa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Louise Turpin takan yi murmushi lokaci zuwa lokaci yayin zaman kotun

''Ni 'yar gwagwarmaya ce, ina da juriya kuma ba na karaya.''

Ta kara da cewa: ''Mahaifina ya sauya mahaifiyata. Sun kusan sauya ni ni ma, sai dai na yi saurin gano abin da ke faruwa.''

Me iyayen ke cewa?

David da Louise Turpin sun zub da hawaye sosai suna neman afuwar yadda suka ci zarafin 'ya'yannasu.

A lokacin da yake jawabi a madadin mahaifin nasu mai shekara 57, lauyan Turpin ya ce: ''Ba ni da niyyar cutar da 'ya'yana kuma na ba su wannan tarbiyar ce da zuciya guda'

''Ban azabtar da su ba kuma ba ni da niyyar cutar da 'ya'yana.

'' Ina matukar sonsu kuma ina da yakinin cewa 'ya'yana na kaunata.''

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

David da Louise Turpin

A lokacin da take yi wa kotu bayani, mahaifiyarsu Louise Turpin mai shekara 50, ta ce a yi mata afuwa kan abubuwan da ta aikata.

''Ina son 'ya'yana sosai,'' ta ce, ''Burina a kullum shi ne na gan su, na rungume su na kuma nemi afuwarsu.''

Asalin hoton, facebook

Bayanan hoto,

Yaran David da Louise Turpin sun shafe shekaru suna fuskantar cin zarafi

Wani irin azabtarwa yaran suka sha?

lokacin da 'yan sanda suka kai sumame gidan yaran da shekarunsu ke tsakanin 2 zuwa 29 na cikin yunwa.

Akwai dansu mai shekara 22 da aka sanyawa mari aka garkame shi a bakin gado. 'Yan uwansa mata biyu kuma an sake su daga dauri.

An haramta musu wanka sama da sau daya a shekara, ba sa iya amfani da makewayi kuma babu wanda aka taba kaiwa wankin hakori.

Asalin hoton, DAVID-LOUISE TURPIN/FACEBOOK

Bayanan hoto,

Da dama daga cikin yaran sun ce sun yafe wa iyayen nasu