Ana zaben kara wa shugaban Masar iko

Shugaba Abdul Fattah al-Sisi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan hamayya na farga kasar za ta koma zamanin mulkin Hosni Mubarak

Al'ummar Masar suna wannan zaben ne na rafaranda ko raba gardama 'yan kwanaki bayan da sauye-sauyen da ake kudurin yi wa kundin tsarin mulkin suka samu amincewar majalisar dokokin kasar da gagarumin rinjaye.

Kawo yanzu dai Shugaba Abdul Fattah al-Sisi bai bayar da wata sanarwa game da gyare-gyaren ko kuri'ar raba gardamar ba.

Shugaban majalisar dokokin kasar dai ya fito karara ya ce, bangaren da ke da rinjaye ne na majalisar ya amince da yin kwaskwarimar.

Wanda daman wannan ba wani abin mamaki ba ne, kasancewar majalisar cike take da masu biyayya ga shugaban, abin da ya sa masu hamayya ke kiransu 'yan amshin Shata ko rakumi da akala.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Majalisar dokokin Masar na cike ne da magoya bayan al-Sisi

Sauye-sauyen dai za su ba wa Shugaba Sisi karin iko kan bangaren shari'a, inda zai samu ikon nada mai gabatar da kara na kasa da kuma manyan alkalai.

Ita dai al'ummar Masar ta tashi tsaye ainun a harkokin siyasa tun bayan juyin-juya hali na 2011.

Abin da ya sa jama'a suka yi cincirundo sosai tsawon sa'o'i a layin jefa kuri'a a zaben shugaban kasa na farko wanda aka shirya shekara daya bayan juyin-juya halin.

Wannan zaben shi ne ya kawo Mohamed Morsi kan mulki, ya zamna shugaba farar hula na farko a kasar.

Shekara daya bayan zuwansa, sai Mr Sisi, wanda a lokacin yake ministan tsaron kasar ya kawar da shi, bayan zanga-zangar gama-gari ta kin jinin mulkinsa.

Wannan ya ba wa gwamnatin Mr Sisi damar bugun kirji da alfahari na dawo da zaman lafiya da aka dade ba a gani ba a Masar.

Wani babban sauyi dangane da wannan zaben raba-gardama shi ne bayar da karin karfin iko ga rundunar sojin kasa ta kasar.

Tsawon shekara da shekaru, sojojin kasar sun kasance masu taka gagarumar rawa a siyasar kasar da kuma tattalin arzikinta.

A yanzu kuma sojin sun zama tamkar masu kula da kuma kare kundin tsarin mulki da kuma mulkin farar-hula na kasar.

Su kuwa masu suka suna ganin wannan ba abin da zai haifar illa kara bude kofa sosai ga mayar da Masar kan salon mulkin soji.