Ana zargin 'yan mata 2 da yunkurin kashe mutum 9

Classroom stock photo

Asalin hoton, Getty Images

'Yan sanda a jihar Florida da ke Amurka sun damke 'yan mata biyu masu shekaru 14 sakamakon zarginsu da yunkurin kashe mutum tara.

An kama 'yan matan ne bayan daya daga cikin malaman makarantarsu ya gano wasu takardu cikin jakarsu da ke bayar da bayanai dalla-dalla kan hanyoyin da za su bi su aiwatar da kisar.

Kamar yadda suka yi bayani a cikin falle takwas na takardun, sun bayyana hanyoyin da za su samu bindigogi da kuma hanyar da za su bi wajen kawar da gawarwakin bayan sun kashe su.

'Yan matan biyu masu shekaru 14 na fuskantar tuhume-tuhume tara na kokarin kisan kai da kuma tuhume-tuhume uku na kokarin garkuwa da mutane.

Malamin makarantar ya bayyana cewa yadda aka yi ya gano cewa akwai lauje cikin nadi a al'amarin yaran shine bayan ya ga yaran sun damu sakamakon rashin ganin jakar da suka saka takardun ba.

Sai yaji daya daga cikin 'yan matan na cewa ''zan fada masu cewa wasa ne ko da kuwa an kiramu ko kuma an gano mu.''

Sai daga baya malamin ya binciko har ya gano jakar.

Takardun kuma sun yi bayani kan yadda matan za su samo makamai da kona hujjoji da kuma birne wadanda suka kashe.

Haka kuma, akwai bayanin irin kayan da za su saka yayin gudanar da wannan danyen aiki da kuma irin kwankwon rufe fuskar da za su maka wa fuskokinsu.