Mene ne dalilin mata na goyon bayan ta'addanci?

Shamima Begum na da shekara 15 a lokacin da ta bar Ingila a 2015

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Shamima Begum na da shekara 15 a lokacin da ta bar Ingila a 2015

Duk lokacin da aka baza labarin mata saboda ta'addanci, abin da aka fi lura da shi, shi ne kimar matsayinsu na wadanda suka jikkata (cutu) ko wadanda aka hada karfi da su wajen shawo kan tashintashina.

In an yi nazari, za a ga cewa matan da ke goyon bayan tsattsauran ra'ayin ta'addanci a wasu lokutan lamari ne da ba a cika lura da shi ba.

Wannan lamari ya samu sauyi ne bayan da wata matashiya 'yar shekara sha wani abu, mai suna Shamima Begun, wadda aka kwatanta a matsayin "'yar riko" a kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Musulunci bayan da aka shawo kanta a sansanin 'yan gudun hijirar Siriya.

Shekaru hudu bayan ta fice daga kasar Birtaniya da kawayenta biyu, sai suka shiga kungiyar ta'addanci ta IS, amma ta yi ikirarin cewa ita kawai, "matar aure ce."

Duk da haka, sakataren harkokin cikin gida na kasar Birtaniya, ya soke mata kimarta na zama 'yar kasar Birtaniya, inda ya nuna cewa: "Idan kin goyi bayan ta'addanci, lallai akwai sakamakon hukuncin aikata hakan."

Tana shirin samun tallafin kariyar shari'a don daukaka kara kan wannan matakin (da aka dauka a kanta).

Mata a kungiyar masu tsattsauran ra'ayi

Halin da Misis Begum ta tsinci kanta ya bijiro da alamar tambaya game da matan da suka yunkura wajen fafutikar ta'addanci a daukacin kungiyar IS da sauran kungiyoyi.

Nazarin cibiyar bincike ta Rusi ya yi nuni da cewa: Kashi 17 cikin 100 na wadanda kungiyar IS ta jefa a fafutikar ta'addanci a Afirka mata ne, yayin da wani binciken daban ya yi nuni da cewa kashi 13 cikin 100 na 'yan kasashen waje da kungiyar IS ta tsunduma su fafutikar ta'addanci a kasashen Iraki da Siriya mata ne.

Hakikanin adadin alkaluman na da rikitarwa domin akwai yiwuwar su haura yadda aka sani.

Asalin hoton, Met Police

Bayanan hoto,

Shamima Begum daga hannun dama da kawayenta na makaranta biyu wato Amira Abase da kuma Kadiza Sultana a filin jirgin sama na Gatwick a 2015

Dimbin nazarin Rusi da sauran masu bincike sun gudanar da bincike kan rawar da mata ke takawa a kungiyoyi irin su IS (kungiyar fafutikakar kafa Daular Musulunci da al-Shabab, kungiyoyi mafi munin tada kayar bayan ta'addanci a Afirka.)

Masu binciken sun gana da mata wadanda kai tsaye ko ta bayan fage suka tsunduma cikin kungiyar al-Shabab, don gano yadda aka yi suka samu kansu, da irin tasirinsu a harkar ta'adanci ga matan.

Aikin binciken ya fito ne daga masana daga kasar Kenya wadanda suka samu gogewa na tsawon lokaci, wajen gano alakarsu da al'ummomin da ke tattare da hadarin aukawa cikin ta'addanci.

Kungiyoyin IS da al-Shabab

Rawar da mata ke takawa ta banbanta tsakanin kungiyoyi

Matan da ke kungiyar al-Shabab sun tasirantu da al'adar zama matan mayakan da 'yan aikin gida.

A wasu lokutan ana amfani da su ne a matsayin matan da ake lalata da su don holewa.

Kuma suna iya jawo masu sababbin 'yan kungiya (wadanda za su shigo a yi yaki da su).

Daya daga irin wadannan binciken da aka gudanar a Kenya ya gano cewa, matan akan yaudare su ne da zimmar za a samar musu aikin yi da tallafin kudi a tsara masu dabarun gudanar da harkokin rayuwa.

Alal misali, Hidaya (ba sunanta na gaskiya kenan ba ), mai dinka tufafi, an shigar da ita kungiyar ta hannun wani da ya yi mata alkawarin zuba jari don bunkasa kasuwancinta.

An yaudareta ta amince ta kai ziyara zuwa kan iyakar yankin, inda daga nan aka yi fasakaurinta zuwa cikin kasar Somaliya.

Asalin hoton, Getty Images

A kungiyar IS, matan da suka shiga, musamman wadanda suka shiga kungiyar ta kafar shafin intanet, sukan yi aiki tukuru wajen yada akidun kungiyar.

Dangane da Shamima Begun kuwa, kasancewarta a kungiyar, IS na ganin sun yi nasarar yada farfaganda, duk da cewa ta nuna cewa dan abin da ta aikata bai taka-kara ya karya ba a Siriya ko bai wuce kula da mijinta da 'ya'yana ba.

Sannan matan a cikin kungiyar IS ana sanya su aikin likitanci da kula da marasa lafiya, tare da gindaya wasu sharuda, yayin da kungiyar ke da 'yan sanda mata da ke kula da tarbiyya da dabi'u.

Ba da dadewa ba, yayin da kungiyar ta rasa karfin ikon fadin kasarta a Iraki da Siriya, ta shirya shirin turo mata a gaba-gaba, kamar yadda take amfani da jaridarta ta al-Naba tana kiran mata su fito jihadi, sannan tana fito da faifan bidiyo wanda a bara ta nuna dimbin mayakan kungiyar a Siriya.

Sai dai bambancin da ke kungiyoyin na kara haifar da rudani yayin da kungiyoyin ke zaburar da junansu.

A kasar Somaliya, inda al-Shabab ke kokarin kafa gwamnatin Musulunci karkashin Shari'ar Islama, an samu rahotanni inda mata ke gaba-gaba wajen kunar bakin wake

Nazari kan hare-haren kunar bakin wake a tsakanin shekarun 2007 zuwa 2016 ya nuna cewa kashi 5 cikin 100 da suka aiwatar da farmakin mata ne.

Bayanan hoto,

Sally-Anne ta zama mai daukar mutane a kungiyar IS inda ta tafi Syria inda ake zaton an kashe ta a wani hari da jirgi mara matuki ya kai a 2017

Sannan haka lamarin yake a wasu sassan Afirka, kamar Najeriya, inda masu tayar da kayar baya a fafutikar Islama na kungiyar Boko Haram kan yi amfani da mata masu harin bom din kunar bakin wake.

Mene ne dalilin mata na shiga kungiyoyin jihadi?

Akwai dalilai da dama da ke jan mata su shiga irin wadannan kungiyoyin.

Lamarin ya kai ga cewa abin da ke ingiza maza shi ke ingiza mata, kamar al'amuran da suka hada da jan ra'ayin akida da fa'idar samun kudi.

Sai dai dabarun da ake tunkarar mata da su musamman, su ne jan ra'ayinsu da cewa za su koma rayuwar al'adar matsayin bambanta jinsuna (matsayin mata da maza daban-daban).

Alal misali, daya daga bincikenmu ya nuna cewa masu jawo mutane cikin kungiyar al-Shabab sukan fake da damar rashin kariyar tsaro ga matasan mata Musulmi, wadanda ke fargabar cewa karatu a manyan makarantu zai kawo musu cikas din yin aure a kan kari.

"Idan na samu mutumin da zai aure ni ya ba ni kariya (kula da ni), mene ne zai sanya in damu kaina da zurfin karatu?" a cewar wata dalibar Jami'ar Nairobi da masu binciken suka tuntuba.

Sauran kuwa an gano cewa al'amuran da suka dauki hankalinsu su ne alkawuran samun aikin yi da kudi da sauran damarmaki a fagen rayuwa.

Amma dai zakulo hakikanin manufarsu ta shiga kungiyoyin na da wahala.

Mata da dama da aka tattauna da su sun yi ikirarin cewa an shigar da su kungiyoyin ne ba a son ransu ba.

Kamar ita Shamima Begum , wasu sun yi ikirarin cewa ba sa yin fafutika a harkokin kungiyar, ko kuma shiga a dama da su ba da son ran su ba, wasu kuwa cewa suka yi tsautsayi ne ya afka musu.

Yayin da wasu ke nuni da cewa akwai yiwuwar tursasasu aka yi suka shiga harkokin kungiyar ta wata siga, inda suka musanta suna da alhakin aikata munanan ayyuka, wannan hanya ce mai alfanu wajen dawo da su cikin al'umma.

Hanyar gyara dabi'a

Akwai dabaru da dama na tarbiyyar gyaran dabi'a ga wadanda suka samu kan su a kungiyoyin a da ko dawo da mayakan kan hanya tagari, amma kadan ne aka tsara su da nufin tarairayar mata.

Masu tsara muhimman dabaru da harkokin tsaro na bukatar tunkarar al'amuran da suka shafi mata don ganin an shawo kan su sun yi watsi da kungiyoyin ta'addanci, ta yadda za a kare aukuwar lamarin da gyaran tarbiyya da dabarun sake dawowarsu cikin al'umma.

Alal misali, da yawansu sun haifi 'ya'ya da mayakan da suka mutu ko suka arce daga fagen daga, yayin da wasunsu ke bukatar tarairayar tarbiya da shawo kan yadda za su shawo kan matsanancin halin da suka tsinci kan su a ciki, kan al'amuran da suka kama daga kan fyade zuwa cin zarafinsu ta hanyar tarawar jima'i.

Yana da matukar muhimmanci gwamnatoci su shawo kan al'amuran da suka shafi matan da suka tsunduma a harkokin kungiyoyin ta'addanci.

Lamarin zai fara ne daga kan yadda za a samar da kyakkyawar fahimta kan bambance-bambancen jinsuna da ke ingiza mata, tare da al'amarin da ke da tasiri kan rayuwarsu.

Yin hakan zai yi matukar taimaka wa al'ummomi su tarairayi hadarin da ake fama da shi, kuma ya taimaka wajen dakilewa ko hana karuwar matan da ke shiga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin ta'addanci.

Dangane da wannan makala

Wannan makala nazarin bincike ne da BBC ta sanya kwararrun masana da ke aiki da wasu cibiyoyi suka gudanar.

Martine Zeuthen, masanin dabi'un mutanen da, da na yanzu da ja-gaban shirin Rusi da Tarayyar Turai ta bai wa tallafin kudi ko kuma daukar dawainiyar kudin gudanar da shi, da manufar kashe karsashin tsattsaurar akidar ta'addanci a Zirin Arewacin nahiyar Afirka

Gayatri Sahgal manajan bincike na shirin Rusi

Cibiyar bincike ta Rusi (Royal United Services Institute) farfajiyar nazari ce mai cin gashin kanta da ke da kwarewar binciken kan harkokin kariyar tsaro.