Sudan: An gano makudan kudade a gidan tsohon shugaba Omar al-Bashir

Omar al-Bashir

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sojoji sun hambarar da Omar al-Bashir bayan watanni ana zanga-zanga

Masu shigar da kara sun ce an gano makudan kudade a gidan tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir, kuma a yanzu ana bincikensa kan karkatar da kudin al'umma.

Jami'an tsaro sun gano daloli da euro da kudin Sudan da jumullarsu ta kai $130m.

An yi wa tsohon shugaban daurin talala a gidansa bayan an cire shi sakamakon zanga-zangar da aka yi.

Rahotanni sun ce a yanzu haka ana tsare da shi a gidan kurkukun Kobar mai matukar tsaro.

Wata majiya a sashin shari'ar kasar ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa an gano wasu jakukuna ne makare da kudi sama da $351,000, da euro miliyan shida ($6.7m) da kudin sudan fam biliyan biyar ($105m) a gidan na sa.

Majiyar ta tabbatar da cewa a yanzu haka ana gudanar da bincike kan al-Bashir, inda ta tabbatarwa Reuters cewa masu shigar da kara za su yi masa tambayoyi a gidan kurkun Kobar.

Wani hoto da gidan radiyon Dabanga na kasar Netherlands ya dauka ya nuna wasu mutane sanye da kayan sojoji suna tsaye kusa da wata jaka dake da alamar cewa makudan kudade ne a ciki.

Kudin wanda gidan radiyon Dabanga yace an nunawa manema labarai, an dura su ne a buhun hatsi mai nauyin kilogram 50.

Sai dai duk da kokarin da ake yi na ganin an hukunta tsohon shugaban, har yanzu alamu na cewa masu zanga-zangar ba su da kwarin gwiwa kan sojoji, a cewar wakilin BBC Alastair Leithead.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanagar na fargabar cewa sojoji za su yi zaman dirshan

'Masu zanga-zanga suna son mulkin farar hula'

Alastair Leithead, BBC News, Khartoum

Jama'a sun ci gaba da yin zaman dirshan a tsakiyar birnin Khartoum, suna masu nuna rashin amincewa da cewa da gaske sojoji suke suna son mika mulki ga gwamnatin farar hula.

A kowace rana sai an bayyana wani sabon mataki da zai nuna da gaske sojojin suke, sai dai babu wasu kwararan shaidu da za su nuna cewa ana cika alkwuran da ake yi wa 'yan kasa.

Har yanzu babu ko da hoto da zai nuna Omar al-Bashir a gidan yari, haka kuma babu wata alama ta cewa manyan sojojin kasar sun ji kiraye-kirayen da 'yan kasar ke yi na cewa su mika wa farar hula mulki.

Mutane za su yi farin ciki da sanarwar cewa ana binciken al-Bashir saboda karkatar da kudade, haka kuma masu zanga-zangar za su ji dadin labarin cewa an gano kudaden ne a gidan sa.

A ranar 11 ga watan Aprilu ne sojoji suka tunbuke Omar al-Bashir, sai dai masu zanga-zanga karkashin kungiyar kwararrun kasar sun sha alwashin ci gaba da kasancewa a kan tituna har sai an mika mulki ga farar hula.

Kotun hukunta masu laifukan yaki ta duniya ICC na neman al-Bashir ruwa a jallo saboda zarginsa da laifukan yaki a yankin Darfur.

Sai dai sojojin kasar sun ce ba za su mika shi ba, maimakon haka za a yi masa shari'a ne a gida.

Uganda za ta iya baiwa hanbarerren shugaban mafaka idan ya nemi hakan, kamar yadda ministan harkokin kasashen waje na kasar Henry Oryem Okello ya shaida wa Reuters.

Wane ne Omar al-Bashir?

Mista Bashir ya jagoranci mulkin Sudan tsawon shekara 30.

Ana zarginsa da shirya laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil'adama a yankin Darfur na yammacin Sudan, wanda a dalilin haka ne kotun ICC ta aike masa sammaci.

Bayan watannin da aka shafe ana zanga-zanga - wadda aka fara sanadin tsadar rayuwa aka kuma yi ta kira ga shugaban don ya yi murabus kan hakan - sai a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu ne aka yi juyin mulkin da ya hambarar da shi.

An samar da kwamitin mika mulki na soji sakamakon hambarar da shi din, kuma an ce kwamitin zai ci gaba da aiki har tsawon shekara biyu zuwa lokacin da za a samar da gwamnatin farar hula.

Hukunci ga tsohon shugaban kasar?

Daga Will Ross, Editan BBC na Afirka

A lokacin mulkinsa na shekara 30, Omar al-Bashir ya daure da yawa daga abokan adawarsa na siyasa a gidan yarin Kobar. A yanzu 'yan uwansa sun ce shi ma can aka kai shi.

Yanayin yadda gidan yarin yake abun kaduwa ne sosai idan aka kwatanta da daular da ke fadar shugaban kasa, inda a can aka yi masa daurin talala tun ranar Alhamis.

'Yan Sudan da dama na fatan a hukunta tsohon shugaban nasu saboda ta'asar da aka tafka a lokacin mulkinsa.

Janar-janar din sojin da a yanzu ke tafiyar da kasar sun ce ba za a mika Mista Bashir ga kotun ICC ba, amma za a yi masa shari'a a Sudan.

Idan har suka ga ga hujja a bayyane cewa yana gidan yari, to masu zanga-zangar da ke neman a dawo da mulkin farar hula za su dan samu kwanciyar hankalin cewa lallai kasar za ta wuce zamanin mulkin kama karya.