Mutune da dama sun mutu harin bama-bamai a Sri Lanka

Bayanan bidiyo,

An kai hare-haren bam a Sri Lanka

Kusan mutum 137 ne aka bayyana sun rasa rayukansu, kuma kusan 300 sun sami raunuka bayan hare-hare bam da aka kai kan wasu coci-coci da otel-otel a Sri Lanka.

An dai sami rahotannin tashi bama-bamai shida, kuma coci-coci guda uku a Kochchikade da Negombo da kuma Batticaloa ne aka kai wa harin a daidai lokacin da ake bukukuwan Easter.

An kuma kai wa otel din Shangri La da na Cinnamon Grand da kuma na Kingsbury hari, kuma dukkan hare-haren sun auku ne a birnin Colombo.

Bikin Easter na cikin manyan bukukuwan mabiya addinin Kirista a kasar.

Hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna yadda bama baman suka lalata daya daga coci-cocin mai suna St Sebastian's a birnin Negombo - inda ya yi kaca-kaca da ginin kuma akwai jini ko ina.

kafafen watsa labarai a kasar na cewa akwai masu yawan bude ido a cikin wadanda harin ya rutsa da su.

Babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin kawo yanzu.