Akalla mutum 300 suka mutu a hare-haren Sri Lanka

Sri Lanka

Asalin hoton, EPA

Ana ci gaba da samun bayanai na sabbin hare-hare da ake kai wa Sri Lanka.

Kusan mutum 300 ne aka tabbatar da mutuwarsu a jerin hare-haren da aka kai a Sri Lanka, yayin da kusan 500 suka jikkata.

Wakilin BBC da ke lardin Colombo ya ruwaito cewa an kara samun wani harin bam a wani otel da ke daura da wani gidan zoo inda a kalla mutane biyu suka rasa ransu.

Rahotanni sun bayanna cewa mutum biyu da aka kashe a harin 'yan sanda ne.

Sai kuma wani sabon hari da aka kai a lardin Dematagoda wanda zuwa hada wannan labarin babu cikakken bayani a kai

Wadannan su ne hare-hare na takwas da aka kai a ranar Lahadi a coci-coci da kuma otel-otel a Sri Lanka da ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 300.

Daga cikin wadanda aka kashe dai akwai 'yan kasashen waje 35, kuma harin ya jikkata mutum sama da 450.

An dai sami rahotannin tashi bama-bamai shida, kuma coci-coci guda uku a Kochchikade da Negombo da kuma Batticaloa ne aka kai wa harin a daidai lokacin da ake bukukuwan Easter.

An kuma kai wa otel din Shangri La da na Cinnamon Grand da kuma na Kingsbury hari, kuma dukkan hare-haren sun auku ne a birnin Colombo.

Sai kuma a yanzu aka kara samun wadannan da ya zama na bakwai na otel din da ke lardin Colombo da kuma na takwas da aka kai a lardin Dematagoda.

A yanzu haka dai gwamnatin kasar ta saka dokar hana fita sakamakon lamarin da ke kara ta'azzara

Asalin hoton, AFP

An kama mutum bakwai

Wakilin BBC Azzam Ameen ya bayyana cewa a yanzu haka an kama mutum bakwai da ake zargi da kitsa hare-haren da aka kai.

Ya bayyana cewa ministan tsaro na kasar ya ce akasarin hare-haren na kunar bakin wake ne da kungiya daya ta shirya.

Sai dai babu wata kungiya da ta fito fili ta dauki nauyin kai harin.

Donald Trump ya jajanta kan harin

Shugaban Amurka Donald Trump ya jajanta kan harin da aka kai a kasar Sri Lanka.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda ya ce kasarsa a shirye ta ke domin ta tallafa.

Asalin hoton, Reuters

Bikin Easter na cikin manyan bukukuwan mabiya addinin Kirista a kasar.

Hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna yadda bama baman suka lalata daya daga coci-cocin mai suna St Sebastian's a birnin Negombo - inda ya yi kaca-kaca da ginin kuma akwai jini ko ina.

Kafafen watsa labarai a kasar na cewa akwai masu yawan bude ido a cikin wadanda harin ya rutsa da su.