To fa! Ashe yin fushi ma abu ne mai kyau?

A very cross-looking grey cat

Asalin hoton, Getty Images

Mafi yawan sassan fadin duniyarmu ana zaune ne cikin lumanar zaman lafiya da wadata.

Kididdigar alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasuwanci ta duniya da gwamnatoci daban-daban a fadin duniya suka tattara sun nuna cewa kasashe da dama talauci na raguwa, sannan tsawon rai na karuwa.

Mafi yawan wadanda ke zaune a kasashen da suka ci gaba suna da kariya, kuma sun samu karuwar dukiya fiye da kowane zamani a tarihin dan Adam.

Shin wane dalili ne ya sanya mutane da yawa ke yin fushi a kodayaushe?

Akwai labaran fusata a kan titi, zazzafar takaddamar kafofin sada zumuntar intanet, a wasu lokutan har 'yan siyasa ke bai wa hammata iska (naushin dambacewa ko kokowa).. a iya yi wa mutum uzuri in har ya dauka cewa duniya ta harzuka da fushi.

Oliver Burkeman - dan jaridar Birtaniya kuma marubucin da ya yi rubutu kan yadda za a samu farin ciki - ya shirya shirin sauya salo, don bin kadin fushi dangane da yadda za a kawo sauyi.

Shin mene ne ke fusata mu? Mene ne ke tunzura lamarin? Ta yiwu mafi muhimmanci shi ne, mummunan abu?

1. Mene ne dalilin harzukar fusatarmu?

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mene ne ke sanyawa a rika bijirowa ko harzuko mana fushi tun a zamanin da, har ta kai ga wani na jin haushin wani har ya fusata?

"Bacin ran da ke harzuka fushi cukurkudadden al'amari ne mai wuyar sha'ani," in ji Aaron Sell, Farfesan nazarin kwakwalwa da nazirin miyagun laifuka a Jami'ar Heidelberg a Ohio, da ke kasar Amurka.

"Don fito da lamarin karara, a iya cewa shi ne linzamin zuciya. Wata hanya ta kutsawa cikin tunanin wani, ta yadda za ka sanya ya kimantaka da daraja. Wata hanya ce ta samun nasarar rikicin da ke tsakaninku, tare da sauya masu tunanin."

Farfesa Sell ya kwatanta yadda muhimmin bangaren "linzamin tunanin zuci" ke bijirowa daga "fuskantar fushi ya kambama tayar da jijiyoyi da hucin hura hanci."

"Kowane daya daga wadannan sauye-sauyen da fushi ke haifarwa a fuska na fito da alamun karfinka/ki da jarumta a zahiri."

A cewar Farfesa Sell, masana kimiyya sun samu kai ga gacin fahimtar cewa " fushin fuska" gadonsa ake yi ba koya ake yi ba, saboda "yara makafi suna bijiro da yanayin fushi da aka saba gani a fuskokinsu."

To ta yaya kyakkyawan "fushin fuska" ya haifar wa magabatanmu nasara (samun rinjaye kan al'amuran rayuwa?

2. Mahangar "sake salon gyaran tarairayar al'amura"

Asalin hoton, Getty Images

Ta yiwu ka ji cewa magabatanmu (kakanin kakanninmu) wadanda ba sa bata rai (yin fushi) har su yi fada sun yi nisan kwana fiye da wadanda suka yi (fushi), amma dai ba haka lamarin ya kasance ba.

"Abin da ya faru, a cewar Farfesa Sell, shi ne, "mutanen da suka damfaru da wani nau'in bacin rai da ke bijiro da fushi sun fi saurin harzukar fusata fiye da wadanda ba sa yi."

Sun yi hakan ne ta hanyar saukaka daidaituwar kyawawan al'amura, har ta kai ga sun yi galaba wajen takaddamar rashin fahimta (ko jayayyar son rai - fifikon ra'ayi)

"A da, mutane wadanda ba sa nuna bacin rai ko fushi a kan tumurmusa su a tauye," in ji Farfesa Sell, wato mutane kan yi musu sata, sannan su wulakanta su, sakamakon haka "sai a kawar da su ko ma a daina jin duriyarsu, sun bata bat."

Wadanda suka tsira su ne wadanda suka yi barazanar janyewa daga hadin gwiwar taimakekeniya (a junansu), inda nan take sukan tunatar da daukacin kyawawan abubuwan da suka aikata, ta yadda sukan sanya mutum dan uwansu ya dawo da baya ya yi ta yaba musu - lamarin da ke haifar da kyakkyawar tarairaya (a tsakanin juna).

Bacin ran nuna fushi shi ya fifita irin wadannan mutane da fifikon bunkasar rayuwa, a cewar Farfesa Sell.

3. Mene ne ke faruwa da jikinmu da zarar mun yi fushi?

Asalin hoton, Getty Images

Don fahimtar fushi muna bukatar yin tunani kan tasirinsa ga jikinmu a zahirance, ta yaya yake zaburar da mu ko kai tsaye yaya tunaninmu ke gushewa.

Farfesa Ryan Martin kwararen mai nazarin lafiyar kwakwalwa a Jami'ar Wisconsin-Green Bay ta Amurka mai bincike ne da ke bibiyar abin da ya danganci fushi, yana gudanar da shirin bin kadin daukacin harzukar fushi na "All the Rage" da ake watsawa ta wani salon sakon rediyon podcast a kowane wata.

"Da zarar kun yi fushi, tsarin sadarwar jijiyoyinku da ke tausasa tarairayar fafata fadanku ko yunkurin fafatawa sai su zabura su fara aiki," a cewar Farfesa Martin, "Bugawar zuciya sai ya karu, numfashinku ya karu, sai ku fara zufa, kuma tsarin sarrafa abincin ku ya rinka tafiya a hankali."

Wannan yamutsin martanin da kwakwalwa ke yi, mataki ne da jiki ke dauka da manufar nuna karfin tunkarar kowane irin rashin adalci da kuke jin an yi maku.

Ita ma kwakalwa na aiwatar da ayyukan ne daki-daki.

"Mun kuma san cewa duk sa'adda mutane suka harzuka da gaske, to tunaninsu zai bijiro a hankali ya rika gudanar da ayyuka daki-daki," a cewar Farfesa Martin, "Sun fi zaburar dabarun tsira" ko "na daukar fansa."

Wannan lamari ne da ke bunkasa shi ma dai ba ku yin tunani kan sauran al'amura lokacin da kuke kokarin daukar mataki kan wani abin da kuke jin ba a kyauta maku ba (an yi ba daidai ba, ko rashin adalci).

4. Mene ne ya sanya rayuwar zamani ke harzuko mana fushi?

Asalin hoton, Getty Images

Akwai tabbacin cewa, mafi yawan mutane, musamman wadanda ke zaune a kasashen da suka ci gaba damuwarsu kadan ce in an kwatanta da magabatansu (kakannin kakanninsu), shi ya sa ake bin bahasin dalilin da ya sanya rayuwar wannan zamanin take cike da harzukar bacin rai da ke tunzura fushi?

Lamarin na da saukin fahimta, a cewar Farfesa Martin: "Mutane al'amura sun sha musu kai, ta yadda suna da dimbin bukatun rayuwa, don haka sakamakon kakarewar harkoki sai a ji matukar rashin dadi."

Saukin lamarin shi ne, a cewar Farfesa Martin: "Al'amura sun sha wa mutan kai ga bukatun rayuwa na karuwa, to sakamakon hakan da mutum ya ji harka ta tsaya cik to al'amura ke nan sun yi matukar muni (a rayuwa)."

Idan ya zama dole mu bi layi a katafaren shagon sayar da kayayyaki ko mun samu tsaiko daga mai kawo mana makamashi, sai kawai mu harzuka da fushi saboda ba mu da lokacin da za mu bata.

Wannan shi ne abin da ya kamata a ce "an kauce masa, tattare da jin cewa ba a iya tabuka komai" al'amarin da ke sanya harzukar fushi (na nuna rashin jin dadi), a cewar Farfesa Martin.

Su ne al'amuran da "ya kamata a kauce musu, don sukan jefa mu cikin halin rashin iya yin katabus" har mu fusata, a cewar Farfsa Martin.

Yadda bacin rai ke bijiro mana da fushi tattare da irin matakin da muke dauka "ba a kodayaushe lamarin ke da alfanu a duniyarmu ta wannan zamanin."

5. Za mu iya shawo kan fushinmu fiye da yadda muke tsammani?

Asalin hoton, Getty Images

Hakika cutar da mutumin da kuke ke fushi da shi ba abu ne mai alfanu ba - don haka akwai bukatar mu san yadda za mu tarairayi fushinmu.

Muna iya shawo kan lamarin fiye da yadda muke zato, a cewar Maya Tamir, Farfesan nazarin kwakwalwa a Jami'ar Hebrew ta Jerusalem.

Sosuwar zukata ba shi da fa'ida tun da bunkasar harzuka yake haifarwa, a cewar Maya, "al'amura ne da ake samun horo a kai, sai mu sauya, mu tasirantu da dabarun sarrafa juya akalar yanayinmu."

Bincikenta ya nuna cewa ba kodayaushe ne fushi ke haifar da rikicin fada ba.

"Mu ba 'yan kore ba ne da ke lilo, inji Maya. "Bacin ran nuna fushi ba ya mayar da mu mafadatan da ba za su iya tarairayar hankalinsu (ko kawunansu ba)."

6. Yin kyakkyawan aiki mai amfani lokacin fushi

Asalin hoton, Getty Images

Bacin rai dai kan iya matukar harzuka mu (cikin dugunzumar fushi) zai iya tunzuro da fada da zage-zage kai har ma takaddamar fada mai zafi a shafin Twitter.

Idan wadanda ke bukatar ganin sun kankane karfin ikonsu da matsayinu suka yi fushi, sakamakon hakan na iya haifar da mummunan al'amari - ko ma a karshe da yaki.

Amma masanan fannin kula da kwakwalwa sun ce zai iya tunkarar tunaninmu, ya kara masa karsashin zaburarwa don daukar mataki lokacin da aka aikata mana ba daidai ba.

Mark Vernon , masanin falsafa (kula da juya akalar tunani) da kula da lafiyar kakwalwa, ya bayyana yadda mutanen da, na zamanin Plato da Aristotle (masanan alkiblar juya akalar tunani) suke da tabbacin cewa akwai abin da ake yi wa lakabi da "fushi mai kyau."

Sai su ji cewa wanda ke cikin fushi zai yi kyau garesu idan lokacin da suke fushin sun sarayar da harzukar fushinsu wajen gudanar da kwakkwaran aiki (mai amfani).

Saboda haka, harzukar fushi dai "tana iya zabuar da mutum ya aikata wani abu gaba-gadi (da kwarin gwiwa kai tsaye) ko ta zaburar da su yi muhawara mai kyau da za ta bayar da damar warwarewa ko shawo kan takaddamar cikin adalci.

Don haka an gano shi cewa: ba za a iya cewa daukacin fushi ba shi da fa'ida.

Kawai abin da muke bukata shi ne tarairayar juya akalar wannan kakkarfan lamari, mai matukar sosa zuciya, ta yadda za a sarayar da shi da kyakkyawan tasiri, don gudun ka da mu karasa da dabaibayin bacin rai da zakuwar kai farmakin fada.