Sudan: Masu zanga-zanga na jiran sanarwar mika mulki ga farar hula

Protesters have continued to stage a sit-in in central Khartoum

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Protesters have continued to stage a sit-in in central Khartoum

Masu zanga-zanga a Sudan na kokarin sanar da majalisar da farar hula za ta jagoranta da suke so ta jagoranci kasar wace za ta kasance a matsayin gwamnatin rikon kwarya bayan hambarar da Omar al-Bashir.

Dubban masu zanga-zangar na ci gaba da haduwa a wajen shelkwatar rundunar sojojin kasar da ke birnin Khartoum.

Shugabannin da ke jagorantar zanga-zangar na ci gaba da tattaunawa da sojojin kasar tun bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.

A ranar Lahadi ne dai sojojin suka bayyana aniyarsu ta ba farar hula mulki, amma suna kokarin kafa majalisar da farar hular za ta jagoranta da taimakon sojojin.

Me shugabannin masu zanga-zangar ke shiryawa?

Kungiyar Sudanese Professionals Association (SPA), ita ce kungiyar da ta jagoranci zanga-zangar da ta yi sanadiyar juyin mulkin hambarar da Omar al-Bashir kuma har a yanzu, ita ce gaba-gaba wajen gudanar da zanga-zanga da kuma tattaunawa da sojojin wajen ganin cewa mulki ya dawo ga farar hula.

Tun a baya dai, daya daga cikin jagoran kungiyar ta SPA ya bayyana cewa wannan zai iya kawo tsaiko wajen bayyana majalisar riko ta farar hula amma ya tabbatar da cewa sanarwar za a yi ta ne a ranar Lahadi a filin da ake gudanar da zanga-zangar.

Masu zanga-zangar na san majalisar rikon ta zamana ita ce za ta ci gaba da gudanar da harkokin gwamanti har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe a kasar.

Me sojojin za su yi?

A ranar Lahadi, sojojin sun amsa da cewa za su amsa kiran da masu zanga-zangar suke yi na mulkin farar hula cikin mako daya inda suka bayyana ra'ayinsu na majalisar ta zamana ta hadaka tsakanin farar hula da sojojin.

Tun tuni dai sojojin ke nuna tirjiya wajen mika mulki ga farar hula inda suka ki bayar da kai domin bori ya hau.

Amma kuma sojojin sun saki wasu daga cikin 'yan siyasar da ke gidan kaso inda kuma a wani bangaren kuma sojojin suka kama wasu daga cikin mukarraban Omar al-Bashir.

Duk da cewa sojojin sun yi alkawarin ba za su kori masu zanga-zangar daga filin da suke gudanar da ita ba, amma sun yi kira garesu da su bari a ci gaba da rayuwa cikin walwala.