Yadda mai barkwanci ya zama shugaban kasa

Volodymyr Zelensky

Asalin hoton, Getty Images

Mai wasan barkwanci a telebijin Volodymyr Zelensky, ya lashe zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Ukraine.

Zelensky, ya samu kuri'u sama da kashi 70 inda ya doke shugaban kasa mai ci Petro Poroshenko.

Tuni dai Poroshenko ya karba shan kaye, amma ya ce ba zai hakura da siyasa ba.

Daga cikin jawabinsa na farko, Zelensky ya ce yana son ya kulla yarjejeniyar tsagaita buda wuta da 'yan aware a gabashin Ukraine.

Ya ce zai ci gaba tatattauna yarjejeniyar Minsk, zuwa bin matakan da suka shafi tabbatar da tsagaita buda wuta.

Amma Wakilin BBC a Kiev ya ce sabon shugaban zai fuskanci kalubale kan yadda zai nunawa 'yan kasar da duniya baki daya cewa ya san me yake yi.

Mista Zelensky wanda sabo ne a siyasa, an fi saninsa da ban dariya a telebijin, inda ya yanzu kwatsam ya zama shugaban kasar Ukraine.