Buhari da wasu shugabanni sun yi Allah wadai da harin Sri Lanka

BBC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu daga cikin shugabannin kasashen duniya masu fada a ji sun yi Allah wadai da harin da aka kai a coci-coci- da otel-otel a Sri Lanka.

Harin dai wanda ya yi sandadiyar mutuwar kusan mutum 300 da raunata sama da mutum 500 ya faru ne a lokacin da ake bikin Easter a ranar Lahadi a kasar.

Hare-haren, wadanda ake zargin 'yan kunar bakin wake ne suka kai su, sun ja hankalin duniya matuka ganin irin asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi cikin lokaci kalilan.

A wani sakon Twitter da mai magana da yawun shugaban Najeriya Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ''amadadin gwamnatin Najeriya da mutanenta, shugaban kasar na ta'zaziyya ga iyalen wadanda aka kashe a lokacin harin kuma yana fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka''

Shi ma Shugaban Amurka Donald Trump, tun bayan faruwar lamarin ya bayyana alhininsa a shafinsa na Twitter inda ya ce Amurka a shirya ta ke da ta bada tallafi.

Ita ma Firai Ministar Ingila Theresa May ta ce harin da aka kai a coci-coci da otel-otel a Sri Lanka abu ne mummuna, inda ta kara bayyana cewa yakamata a tashi tsaye domin ganin cewa kowa ya ci gaba da yin bautarsa cikin natsuwa ba tare da fargaba ba.

Tun bayan afkuwar lamarin, shugabannin kasashe da dama na duniya na ci gaba da ta'aziyya da kuma yin Allah wadai da hare-haren da aka kai a kasar.

Wasu daga cikin hotuna bayan harin

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, EPA