Amurka za ta hukunta kasar da ta sayi man kasar Iran

Jirgin dakon mai

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Takunkumin zai ya jawo mummunar barna ga tattalin arzikin Iran

Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai sanya takunkumi ga duk kasar da ta ci gaba da sayan man fetur din kasar Iran.

Fadar White House ta ce wa'adin da ta dauka wa kasashen China, India, Japan, South Korea da kuma Turkey zai kare a watan Mayu, inda za su fuskanci hukunci idan suka ci gaba da sayan man.

An dauki matakin ne domin a gurgunta harkokin cinikayyar man kasar ta Iran baki daya, wadda ita ce babbar hanyar samun kudaden-shiga ga kasar.

Iran ta hakikance kan cewa takunkumin ba ya kan doka kuma "ba ta dauke shi da wani muhimmanci ba".

Mista Trump ya sake saka takunkumin ne a shekarar bara bayan ya fitar da kasarsa daga yarjejeniyar makamin nukiliya tsakanin Iran da kuma manyan kasashen duniya guda shida.

A karkashin yarjejeniyar, Iran za ta kayyade aikace-aikacen sarrafa makamin nukiliya da take yi kuma ta kyale masu sa-ido na kasashen duniya su bincika, inda ita kuma za a sassauta mata takunkumi.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mike Pompeo ya ce Amurka na son ta kara matsa wa Iran don ta mika wuya

Gwamnatin Trump dai tana so ne ta tilasta wa Iran shiga wata sabuwar tattaunawa, wadda za ta hada da maganar makamai masu cin dogon zango da take kerawa da kuma 'aikace-aikacen taimaka wa 'yan ta'adda" a Gabas Ta Tsakiya".

Takunkumin dai ya jawo mummunar barna ga tattalin arzikin Iran din, wanda hakan ya karya darajar kudin kasar, ya jawo hauhawar farashin kaya sannan kuma masu zuba jari da dama suka fice daga kasar.

Me kasashen da abin ya shafa ke cewa?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ministan harkokin kasashen waje na kasar Turkey Mevlut Cavusoglu ya ce yunkurin na Amurka "ba zai kawo zaman lafiya ba kuma zai yi wa al'ummar Iran illa".

"Kasar Turkey ta yi watsi da takunkumin da kuma katsalandan game da yadda ya kamata kasashe ya kamata su yi hulda tsakaninsu," in ji shi.

Ita ma kasar China Allah-wadai ta yi da hukuncin.

"Hulda tsakanin China da Iran abu ne a fili kuma bai saba wata doka ba, ya kamata a girmama hakan," kamar yadda aka ruwaito Geng Shuang, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar ya fada.

Jaridar Financial Times ta ruwaito sakataren gwamnatin kasar Japan yana cewa bai kamata a samu wata tangarda ba game da ayyukan kamfunan kasar ba.

Kasar Indiya kuwa tana ci gaba da nazartar tasirin takunkumin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na PTI ya ruwaito cewa kasar za ta so ta kawo karshen huldar ne a hankali.

Ita kuwa kasar Korea Ta Kudu ta dena sayan man kasar ta Iran na tsawon wata hudu, amma ta ci gaba da saya a watan Janairu da ya gabata.

A watan Maris kadai ta sayi man fetur da ya kai 284,600 bpd.