Buhari: 'Ba na yin barci a bakin aiki'

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani ga Bishop na Yola Stephen Mamza wanda ya ce ci gaba da kashe-kashen da ake yi a kasar wata manuniya ce ga "yadda shugaban yake barci a bakin aikinsa."

Shugaban ya mayar da martanin ne ta bakin babban mai taimaka masa a fannin yada labarai Malam Garba Shehu a ranar Litinin.

A lokacin wa'azinsa na bikin Easter, Bishop Mamza, ya soki gwamnatin Buhari kan yadda ta kasa kawo karshen kashe-kashe da satar mutane don neman kudin fansa.

Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Babban Limamin Katolika na Yola bai yi ya Shugaba Buhari adalci ba, inda ya ce "an samu ci gaba sosai a shekaru uku zuwa hudu da suka gabata a ciki da wajen garin Yola."

Ya ci gaba da cewa:"Wannan ci gaban da aka samu ba zai yiwu ba, idan da a ce shugaban bacci yake yi."

Ya ce "kimainin 'yan gudun hijira 400,000 da ke samun mafaka a Adamawa yanzu sun koma Borno - abin da ya sa aka samu dimbin fitowar masu kada kuri'a a yankin Arewa maso Gabas lokacin zabe."

Har ila yau ya ce: "Bayan garin Yola, garuruwan Michika da Madagali da Mubi wadanda a baya suke karkashin ikon Boko Haram, tuni suka dawo hannun dakarun sojin Najeriya."

A karshe Malam Garba Shehu ya ce "yankin Arewa maso Gabashin kasar ya samu ci gaba fiye da yadda yake a lokacin gwamnatin baya."