Za a fara gwajin riga-kafin Maleriya a karon farko a Malawi

Ana yin allurar riga-kafi

Asalin hoton, D Poland/PATH

Bayanan hoto,

Tuni aka fara yin gwajin allurar

A wani yunkuri na kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro wato Maleriya, an fara gudanar da allurar riga-kafin cutar ta farko ga yara a kasar Malawi.

An samar da sabuwar riga-kafin ta RTS wadda za ta taimaka wa garkuwar jikin dan Adam ta yadda zai ya ki cutar da kansa, wadda cizon sauro ke haifarwa.

Zazzabin Maleriya mai nacin tsiya, ya sake kunno kai ne bayan shekara guda aka samu nasarar ganin bayansa.

"Wannan wata babbar nasara ce ga allurar kan cutar ta Maleriya da kuma lafiyar al'umma baki daya," kamar yadda Dakta kate O'Brien daraktan riga-kafi na hukumar lafiya ta duniya WHO ya shaida wa BBC.

Alkaluma na baya-bayan nan sun nuna cewa zazzabin Maleriya ba raguwa yake ba, wanda hakan yake kawo damuwa game da yadda yake ci gaba da yaduwa.

Kasar Malawi ce kasa ta farko da aka zaba don yin gwajin riga-kafin.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ana sa ran za a yi wa yara 120,000 masu shekara biyu zuwa kasa allurar.

Kasashe Ghana da Kenya za su kaddamar da ita ne a 'yan makonni masu zuwa.

An zabi kasashen uku ne saboda sun yi kokarin kawo karshen cutar wanda suka hada da yin amfani da ragar sauro, sai dai duk da haka cutar na nan.

Yaya girman cutar take?

Zazzabin Maleriya yana kashe mutum 435,000 a fadin duniya duk shekara, mafi yawansu kananan yara.

Akasarin mace-macen suna faruwa ne a nahiyar Afirka.

Yara sama da 250,000 ke mutuwa kowace shekara a nahiyar ta Afirka, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana.

Dakta O'Brien ya ce "Maleriya babbar cuta ce da ba ta jin magani wadda kuma da wuya a samar da riga-kafinta".

An fara gwajin riga-kafinta ne a shekarar 2009.

Wane tasiri riga-kafin zai yi?

An shafe shekara fiye da 30 wajen samar da samfurin riga-kafin na RTS,S, wanda kamfanin GSK ya samar a shekarar 1987.

An yi ittifakin an kashe kudi har dala biliyan 1 kafin a kawo inda ake a yanzu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Campaigners have long been calling for an effective way to deal with malaria

"Babu wanda yake tunanin cewa riga-kafin zai yi magani nan take," in ji Dakta Schellenberg

Ya kara da cewa: "Ba lallai ne a dauki abin da muhimmancin gaske ba, amma muna maganar ragin kashi 40 cikin 100 na cutar ne wadda har yanzu take kashe mutane ko da kuwa kana da tsarin kiwon lafiya mai kyau."

Dakta O'Brien shi kuwa cewa ya yi za a fi yi wa jarirai riga-kafin sabobda sun fi zama cikin hatsari.

Ana sa ran za a gama wannan zagayen na riga-kafin a shekarar 2023, kamar yadda Path ta bayyana.