Ko kun san illolin tiyatar gyaran jiki?

  • Daga Adam Eley da Pete Walker
  • BBC Victoria Derbyshire programme
Rachael Knappier ta kara girman labbanta

Asalin hoton, Rachael Knappier

Bayanan hoto,

An yi ta kiraye-kirayen tsaurara dokoki kan yi wa halittar jiki kwaskwarima kamar kara girman labba

Za a kaddamar da wani shirin kawo karshen sauya halittar jiki ba ta hanyar kwararru ba a kasar Ingila.

Wannan ya biyo bayan yadda mutane ke kara sha'awar yin tiyatar, kamar mazaunai na boge wato "Brazilian butt", wanda ya jawo rasa ran mutane masu yawa.

Akwai kuma gargadi a kan yawaitar amfani da sinadarai wajen yin kwaskwarima ga fuska da kuma kara girman labba, wanda hakan ke jawo rudani mai yawa wanda hukumar lafiya ta NHS ce kawai ke iya magancewa.

Kwararru sun yi maraba da shirin, amma sun yi kira da a sanya wasu dokoki.

Sashen kiwon lafiya na Ingila ya shaida wa shirin BBC na Victoria Derbyshire cewa, shirin wanda za a kaddamar makonni masu zuwa, zai tabbatar cewa an fadakar da mutane sosai game da amfanin neman bayanan masana game da karin girman labba, mazaunai da kuma tiyatar gyaran jiki.

Sashen ya ce kuma yana fatan dakile masu yin karambanin gyaran jikin saboda illar da yake haifarwa ga lafiyar kwakwalwa da kuma jikin mutum, da kuma dimbin kudin da hukumar NHS take kashewa wajen kula da masu yinsa bayan sun yi.

Nora Nugent likita ce kuma mamba a kungiyar British Association of Aesthetic Plastic Surgeons, ta ce ta yi maraba da shirin na gwamnati.

Ta ce karuwar yawan masu sha'awar tiyatar gyaran jiki yana da nasaba da rashin ilimin abin da ka iya faruwa yayin da kuma bayan tiyatar.

Duk da cewa karuwar ta samo asali ne daga yadda taurarin fina-finai ke tallata yadda suka yi ta su, Nora Nugen ta ce "tana kuma da nasaba da tallace-tallace da kuma saukin kudin gudanarwa".

Wannan ya biyo bayan wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da BBC da Deltapoll suka gudanar a shirin Victoria Derbyshire da Newsbeat, wanda ya nuna cewa kashi 83% na mata 1,033 masu shakara 18 zuwa 30 za su yi tiyatar idan suna da kudi sannan kuma babu matsala ga lafiyarsu.

Kashi 63% daga cikinsu sun ce za su yi wa tumbinsu kwaskwarima, inda kashi 53% kuma za su yi gyara mamansu.

Daga cikin kashi 7% na wadanda suka canza halittar labbansu, wadanda kuma aka yi binciken a kansu:

  • kashi 69% suna da kwarin guiwa a kan canjin
  • kashi 52% sun ji cewa sun kara kyau
  • kashi 24% sun ji cewa sun rage kyau
Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

'An lalata min fuska'

Wani mai suna Greg (ba sunansa na ainahi ba ne) ya shaida wa BBC cewa ya zama jiki amfani da yi wa kansa allura don kara girman labbansa da kumatu.

Ya saye su ne ta Intanet, kuma take ya fara yi wa kansa allura da su shekara uku da suka gabata.

"Tsaf za ka manta da yadda fuskarka take a baya," ya bayyana.

"Akwai wani lokaci na rika yi akai-akai har mahaifiyata na cewa fuskata ta lalace kuma ina fita daga siffata ta asali."

Ba lallai sai kana da ilimin kiyon lafiya ba, za ka iya yin allurar saboda ba ta da wata ka'ida kamar kwayoyin magani.

Sai dai masu yi wa kansu allurar za su iya fuskantar kumburi da kuma harbuwa da cuta, wadanda sai an sha magani ko kuma ma tiyata kafin a warke.

Kuma sukan haddasa rauni ga fata har ma da makanta.

'Akwai ciwo sosai'

Greg ya taba yin kuskure wajen yi wa kansa allurar kara girman labba.

"Na farka washe gari na gan su daban-daban - daya ya fi daya girma," in ji shi.

"Na samu kumburi kuma abin yana da matukar ciwo.

"Sai da na ji kunyar wajen neman taimako."

Greg ya ce a yanzu zai iya bai wa mutane shawarar kada su yi amfani da ita saboda "abu ne mai hatsari".

"In ka san hatsarin da ke tattare da hakan dole ne ka kiyaye."

Misis Nugent kwararriyar likitar tiyata ce, kuma ta ce tana da damuwa game da masu yi wa mutane allurar musamman masu sana'ar kwalliya, wadanda ba su da kwarewa a likitance.

Wannan yana jawo hatsari in ji ta, ta kuma kara da cewa da yawa ba su cancanci su duba maras lafiya ba ko kuma su gane wata matsala idan ta taso.

Ta yi kira da a kayyade wadanda za su iya gudanar da allurar.

Sashen Lafiya ya ce: "Duk wanda ke da sha'awar a yi masa tiyatar gyran jiki ya tabbatar ya nemi kwararre kuma amintaccen likita, kuma ya tabbatar ya fahimci hatsarin da ke ciki game da lafiyar jikinsa da ta kwakwalwarsa.

"Muna kokarin bunkasa harkar tiyatar ta hanyar bayar da horo da kuma bayanai ta yadda mutane za su iya daukar matakin da ya dace game da rayuwarsu."

A watan Maris gwamnatin yankin Wales ta ce "ya kamata nan gaba" neman lasisin kiyon lafiya ya kunshi har da yin allurar gyaran jiki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Taurari irinsu Kylie Jenner ta taimaka wajen yada gyaran labba

Save Face wata hanyar tattara bayanai ce kan amintattun likitoci, kuma ta ce ta samu korafe-korafe har 934 daga marasa lafiya game da likitocin da ba su da rajista. 616 daga cikinsu suna da alaka da gyaran labba.

Misis Nugent ta ce har wa yau, tana da damuwa game da masu fita kasar waje don neman tiyatar gyaran jikin, inda ba su fiya ganin likitan ba har sai a ranar da za a yi tiyatar.

Hakan yana jawo rikici sosai wajen bibiyar lafiyarsu saboda rashin isassun bayanan marasa lafiyar.

Ta ce wannan ya hada da kara girman mazunai wato "Brazilian butt lift", wanda ya jawo rasa ran mata biyu 'yan Birtaniya.