Limaman Saudiyya za su ja sallar asham a kasashe 35

sallah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shirin wani kokari na masarautar don nuna kulawa da tallafawa dukkan musulmai a duk inda suke

Ministan harkokin addinin musulunci na Saudiyya Abdullatif Al-Asheikh, ya amince da tura tawagar limamai 70 don jagorantar sallolin Tarawih (asham) da Tahajjud a kasashe 35 na duniya a lokacin azumin Ramadan.

Dama dai ma'aikatar ta saba aika limamai wasu kasashen lokacin azumi don jagorantar sallolin da kuma wayar wa da musulmai kai dangane da abun da ya shafi addini.

Jaridar Saudi Gazeete ta ruwaito ministan yana cewa hakan wani bangare ne na kokarin masarautar don nuna kulawa da tallafawa dukkan musulmai a duk inda suke.

Ya ce limaman za su dora al'ummar musulmai kan turba ta gaskiya, su bayyana musu ainihin sakon musulunci na gaskiya su kuma wayar musu da kai kan duk abun da ya shafi rayuwar musulmi.

"An zabi malaman ne daga kwalejojin Shari'ah. Dukkansu mahaddatan Al-Kur'ani mai girma ne kuma masana sosai a addinin," in ji shi.

"Wadannan matasan malamai kwararrun masu wa'azi ne wadanda za su iya yi wa Musulmai bayanin addinin Musulunci sosai, kuma za su iya karanto Al-Kur'ani da ka," in ji shi.

Al-Asheikh ya ce masallatan kan cika makil da masu ibadah a lokacin azumi don haka babbar dama ce ga limaman su tafiyar da lokacinsu wajen amfanar mutane da wayar musu da kai.

Asalin hoton, Saudi Gazette

Bayanan hoto,

Ministan yayin da yake ganawa da malaman

"Limaman za su isar da sakon Musulunci da kuma karfafa danganta tsakanin Masarautar Saudiyya da kasashen da aka tura malaman," a cewarsa.

A ranar Litinin ne ministan ya gana da limaman ya kuma umarce su su zamo wakilai nagari ga kasarsu.

Ma'aikatar ta shirya musu wani taron karawa juna sani don kara wayar da kansu kan hanyoyin da ya kamata su bi wajen yada sakon musulunci a kasashen waje.