Donald Trump zai kai ziyara Birtaniya a watan Yuni

The Queen walks alongside Donald Trump as the US President inspects the guard of honour during a welcome ceremony at Windsor Castle on 13 July 2018

Asalin hoton, Getty Images

Fadar Buckingham ta sanar da cewa Shugaban Amurka Donald Trump zai kai wata babbar ziyara ta kwana uku zuwa Birtaniya daga 3 - 5 ga watan Yuni.

Shugaban na Amurka da uwargidansa Melania Trump za su kasance bakin Sarauniya Elizabeth II a yayin bikin na 75 na tunawa da ranar tunawa da Yakin Duniya na Biyu a Portsmouth.

Daga baya zai tattauna da Firai ministar Birtaniya a Downing Street.

Mista Trump ya taba saduwa da Sarauniyar a Fadar Windsor Castle lokacin wata ziyarar aiki da ya kai can a watan Yulin 2018.

Fadar White House ta sanar da cewa wannan ziyarar da shugaban zai kai za ta "tabbatar da dangantaka ta musamman da ke tsakanin Amurka da Birtaniya".

Firai ministar Birtaniya Theresa May ce ta yi wa shugaban alkawarin za ta ba shi damar kawo irin wannan ziyarar bayan da aka zabe shi a 2016, amma ba a sanya rana ba.

Amma ba kowa ne ke murna da wannan ziyara da shugaban na Amurka zai kai Birtaniya ba.

Ministar da ke sa ido ta harkokin kasashen waje daga bangaren jam'iyyar adawa ta Labour, Emily Thornberry ta nuna damuwarta kan ziyarar:

"A ranar da wannan mutumin ke neman yin watsi da wani kudurin Majalisar Dinkin Duniya kan amfani da fyade a matsayin matakin yaki, Misis May ta gayyace shi ya zo nan a karrama shi.

Asalin hoton, GEOFF PUGH/ AFP/ Getty images

Bayanan hoto,

Uwargida Melania Trump da maigidanta Donald tare da firai ministar Birtaniya Theresa May

Shugaban na Amurka da uwargidansa Melania za tafi Faransa bayan wanann ziyarar domin ci gaba da bikin na ranar tunawa da Yakin Duniya na Biyu.

Asalin hoton, Ben Tavener/ BBC

Bayanan hoto,

Hoton wani katon mutum-mutumi na roba da wadanda ke adawa da siyasar Mista Trump suka hada a yayin wata ziyarar da ya kai Ingila a bara.

A shekarar 2011, Sarauniya Elizabeth ta karbi bakuncin Shugaba Barack Obama zuwa Fadar Buckingham a 2011.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

A shekarar 2011, Sarauniya Elizabeth ta karbi bakuncin Shugaba Barack Obama