Yadda wata mata ta yi sumar tsawon shekara 27

Rauni a kwakwalwa na jefa mutum cikin yanayi na dogon suma

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto,

Rauni a kwakwalwa na jefa mutum cikin yanayi na dogon suma

Wata mata 'yar kasar Hadaddiyar Daular Labarawa (UAE) ta farfado daga doguwar sumar da ta yi bayan gamuwa da mummunan hadari mota a shekarar 1991.

Matar mai shekara 32 a lokacin faruwar hadarin, Munira Abdulla, ta samu rauni a kwakwalwarta bayan motar da take ciki ta yi karo da wata bas a hanyarta ta zuwa dauko danta daga makaranta.

Omar Webair, wanda shekarunsa ba su wuce hudu ba a lokacin, na zaune a bayan motar tare da mahaifiyarsa, sai dai bai wani jigata ba, kuma mahaifiyar tasa na rungume da shi.

Direban motar wanda siriki ne ga Munira shi ma ya samu munanan raunuka, a shekarar da ta gabata ya farfado a wani asbibiti da ke Jamus.

Omar ya bayyana yadda hadarin ya auku da kuma yanayin lafiyar mahaifiyarsa, da ci gaba da ake samu wajen ba ta kulawa a wata hira da ya yi da jaridar The National ta Hadaddiyar Daular Larabawa.

'Ta rungume ni domin ba ni kariya'

''Ban taba karaya ba domin a kullum ina da gwarin gwiwar cewa za ta farka,'' kalaman Omar ke nan a zantawarsa da 'yan jarida.

''Dalilin da ya sa na bai wa duniya wannan labari shi ne don na sanar da mutane cewa kar su karaya a kan masoyansu; kar ku yi musu kallon matattu idan suna cikin irin wannan yanayin,'' in ji Omar.

''Mahaifiyata na zaune rike da ni a kujerar baya. Lokacin da ta hango wannan hadari, ta rungume ni domin ta kare ni.''

Babu abin da ya same shi, dan kujewa kawai ya samu a kai, amma mahaifiyarsa ta shafe sa'o'i ba ta samu wata kulawa ba.

An kwashe shekaru ana mata magani

An garzaya da Munira Abdulla asibiti, kafin daga bisani a kai ta wani asibiti da ke London. A can likitoci suka bayyana girman matsalar da halin da take ciki, ba ta jin komai.

Daga can aka mayar da ita birnin Al Ain na UAE da ke kan iyaka da Oman, kuma an sha sauya mata asibiti.

Ta shafe shekaru a haka, tana karban abinci ta hanci, a haka ta ci gaba da rayuwa. Ana mata gashin kashi domin tabbatar da cewa gabobinta da kasusuwanta ba su samu matsala ba.

A shekarar 2017, iyalanta suka samu tallafin gwamnatin, hakan ya ba su damar mayar da ita wani asibiti da ke kasar Jamus.

A can, ta samu karin kulawa ta musamman da magunguna da suka sake taimaka mata wajen samun lafiya.

Rayuwa a asibiti

Bayan shekara guda, musu ya kaure tsakanin dan Munira da wasu mutane a dakin da aka kwantar da ita, a lokacin hayaniyar sai da mahaifiyar ta dan motsa.

''An samu sabanni a dakin da aka kwantar da ita kuma ta fahimci ina cikin hatsari, hakan ya sa tayi motsi.'' a cewar Omar.

''Tana ta motsi cikin yanayi na mamaki, na ruga da gudu na kira likitoci domin su duba ta, sai suka ce komai lafiya.

''Bayan 'yan kwanaki, na farka daga bacci kawai sai na ji ana kiran sunana.

''Ita ce! Ita ce take kiran sunana, na yi tsalle cikin farin ciki; ban taba mafarkin faruwar haka ba a tsawon shekaru, kuma sunana ne kalmar farko da ta ambato.''

Ta kasance ta na jin komai, tana jin radadi kuma ana hira da ita.

An mayar da ita Abu Dhabi, inda ake mata gashin kashi da wasu magunguna - wandanda za su inganta yanayin lafiyarta.

Ba kasaifai ake samu irin wannan yanayin ba

Mutane kalilan kididiga ta nuna kan farfadowa daga dogon suma bayan shafe tsawon shekaru- ko da kuwa an farfado, samun waraka kan dan tsawon lokaci.

Hukumomin lafiya a Birtaniya sun ce abu ne mai wuya a iya yin hasashe kan mutumin da ya tsinci kansa a irin wannan yanayi.

Mutanen da suka farfado daga dogon suma akasari na samun matsalolin nakasa da kwakwalwa ke haifarwa.