Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 60 a Afirka ta Kudu

Wani gida daya rushe a gabar ruwa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ruwan sama ya haifar da zabtarewar kasa da lalata dukiyoyi da tittuna

An samu ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu da kuma yankin KwaZulu-Natal, inda akalla mutum 60 suka mutu.

Cikin mamatan akwai jariri dan wata shida da wani karamin yaro.

Shugaba Cyril Ramaphosa da ya ziyarci yankunan da ambaliyar ta shafa ya ce fiye da mutum dubu daya suka rasa muhallansu.

An shafe kwanaki ana tafka ruwa kamar da bakin-kwarya a yankunan kudanci da gabashin kasar.

An kuma yi hasashe ci gaba da samun ambaliyar da iska mai karfin gaske a yankunan da ke gabar ruwa, haka nan kuma ana sake gargadin mutane.

Ambaliyar ta kassara kasuwanci, gidaje da lalata jami'o'i akalla biyu - daruruwan mutane sun rasa muhallansu.

Bayanan hoto,

Mutane na jajantawa junansu sakamakon iftila'in

Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa na ziyarta 'yan uwa da iyalan wadanda ambaliyar ta rutsa da su.

Wakilin BBC Nomsa Maseko ya ruwaito cewa shugaba ya aza furenni a wani wuri da mutum takwas suka mutu.

An kuma hango yadda yake ture dogarawansa da suka yi kokari hana mutane su yi masa magana.

''Yana muhimmanci a zo a ga abin da ya faru. Mun mika ta'aziyarmu ga 'yan uwa wadanda suka mutu a wannan iftila'i. Mun yi takaicin faruwar wannan al'amari. Irin wannan matuwa akwai kaduwa, musamman ga wadanda ya zo wa da ba za ta,'' a cewar shugaban kasar.

Bayanan hoto,

Mutane da dama suka mutu bayan zabtarewar kasa

Kafin ziyarar ta ranar Laraba, shugaban ya fitar da wata sanarwar da ke cewa: ''Wannan yanayi da ake ciki na bukatar kowanne bangare ya yi aiki tukuru domin kai wa wadanda ambaliyar ta shafa tallafi.''

Ministan larduna, Nomusa Dube-Ncube ta shaida wa gidan rediyon SAFM cewa jami'ai na ci gaba da kiyasta adadin asarar da aka tafka.

Ta kuma bayyana cewa akwai yiwuwar dole a sauya wa wasu matsugunai.

Mutane da dama ne aka kai asibiti kuma tawagar masu bincike da aikin ceto na ci gaba da laluben gano wadanda suke da sauran rai ko baraguzan gini suka danne.