Kalli bidiyon yadda barayi ke satar na'urar ATM

Kalli bidiyon yadda barayi ke satar na'urar ATM

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon:

Wata babbar mota ta ruguza wani gini a wani gidan man fetur da ke Burtaniya inda ta yi awon gaba da na'urar fitar da kudi ta ATM.

Wannan za a iya cewa wata sabuwar fasaha ce da barayi suke amfani da ita domin satar na'urar.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, da zarar sun yi amfani da babbar motar sun ruguza ginin, motar sai ta sungumi na'urar ta saka ta cikin wata motar domin yin awon gaba da ita.

Al'amarin ya faru ne a garin Dungiven da ke Arewacin Ireland.