Shin Najeriya tana da isassun likitoci?

Chris Ngige

Asalin hoton, Federal Government Nigeria

Bayanan hoto,

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Dokta Chris Ngige

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya Chris Ngige ya ce ba shi da wata damuwa game da yadda likitocin kasar suke yin kaura zuwa kasashen waje don neman ayyuka.

Ministan yana wannan batu ne a lokacin da ya yi wata hira a shirin Sunerise Daily na kafar talabijin ta Channels TV a ranar Laraba.

"Ba na damuwa, muna da likitoci fiye da yadda muke bukata. Idan kana da wannan adadi, za ka iya barin likitoci su bar kasar ba tare da wata matsala ba. 'Yan Indiya ne suka koyar da ni darasin kimiyya," in ji shi.

"Likitocin da muke da su sun wuce adadin da muke bukata. Muna da ma'aikatan fannin jinya da yawa a wannan kasa. Ina da tabbaci game da hakan. Muna da su da dama, da dama," a cewarsa.

Sai dai kungiyar likitoci ta kasar (NMA) ta musanta hakan, inda ta ce "akwai karantar likitoci sosai a fannin kiwon lafiyar kasar."

Shugaban kungiyar NMA Dokta Adedayo Faduyile ya kalubanci ministan, inda ya ce duk da cewa shi ma ministan tsohon likita ne, yaushe rabonsa da ya duba marasa lafiya.

"Ya kamata ne a ce likita guda ya rika duba mutum 600, amma sabanin hakan yanzu a Najeriya likita daya yana duba mutum 6,000 ne," in ji Dokta Adedayo.

'Yan kasar da dama ne suka rika bayyana ra'ayoyinsu game da wannan kalamai na ministan a kafafen sada zumunta a ranar Laraba.

Me kididdiga ke cewa?

A wani rahoton baya-bayan nan daga gidauniyar Mo Ibrahim Foundation, ya nuna cewa kasashe a Afirka na kashe daga dala dubu 21 zuwa dala dubu 59 wajen horar da likita guda daya.

Najeriya tana daya daga cikin wadanda aka bayyana a rahoton ta yi asarar dala biliyan 2 tun shekarar 2010 wajen horar da likitoci, wadan da suka yi kaura daga baya.

Ya kuma bayyana cewa nahiyar Afirka tana asarar kusan dala biliyan 2 kowace shekara a fannin kiwon lafiya saboda kaurar likitoci zuwa sauran nahiyoyi.