Me Buhari zai je yi Birtaniya?

FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai je kasar Birtaniya domin kai ziyara ta kashin kansa bayan ya kaddamar da ayyuka a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar a ranar Alhamis.

A wata sanarwa da mai ba shugaban kasar shawara kan watsa labarai Femi Adesina ya fitar, ta bayyana cewa shugaban zai kaddamar da ayyukan ci gaba a fannonin ilimi da lafiya da hanyoyi, bayan nan ne kuma zai kama hanyarsa zuwa Birtaniya.

Wannan tafiyar ta shugaban na zuwa ne kwana guda bayan ya kaddamar da wasu ayyuka a jihar Legas.

Sanarwar dai ta bayyana cewa shugaban zai dawo Najeriyar ne a ranar 5 ga watan Mayun 2019 - wato tsawon kwana 10 ke nan.

Sai dai sanarwar bata bayyana takaimaiman abinda zai kai shugaban Birtaniya ba.

A kwanakin baya ne dai shugaban ya kai ziyara a kasashen gabas ta tsakiya inda har ya gabatar ta makala mai taken "shimfida hanyar zuba jari domin habbaka tattalin arzikin duniya a zamanance."

Haka ma, kwanaki biyu kafin tafiyarsa zuwa kasashen gabas ta tsakiya, shugaban ya je kasar Senegal, inda ya halarci bikin rantsar da Shugaban kasar Macky Sall a karo na biyu.

A shekarar 2017 ne dai shugaban ya kwashe fiye da wata uku a kasar Birtaniya yana jinya, inda a lokacin Mataimakinsa Yemi Osinbajo ya jagoranci kasar a matsayin mukaddashin shugaba.