Mike Zhang: Hotunan nadin sarautar Wakilin 'Yan China a Kano
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya nada wani dan China, Mista Mike Zhang, a matsayin Wakilin 'Yan Chinan Kano ranar Alhamis.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ne ya nada Mista Mike sarautar a fadarsa ranar Alhamis
Dimbin jama'a ne suka halarci taron nakin sarautar
Mike Zhang ya shafe shekara 17 yana harkokin kasuwanci a Kano, kuma shi ne wanda ya mallaki kamfanin ruwan roba na Maya a Kano
Sarkin ya ce ya nada shi sarautar ne saboda "kokarinsa wajen habbaka" kasuwanci a Kano
Sarkin ya ce yana fatan nadin zai kara karfafa masa gwiwa
Ana saran Mista Zhang zai rika halartar zaman fada da kuma sukuwa lokacin hawan sallah
Cikin mutanen da suka samu damar halartar taron nadin sarautar har da 'yan uwansa 'yan China
Har ila yau Sarkin ya ce yana fatan Mista Zhang zai zama" idonsu" tsakanin 'yan kasuwan Kano da 'yan China
Akwai dimbin 'yan China da suke gudanar da harkokin kasuwanci a jihar