Netanyahu zai mayar da sunan wani gari Trump a Isra’ila

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana kudurinsa na sanyawa wani bangare na Tuddan Golan sunan Shugaban Amurka Donald Trump.

Mista Netanyahu ya ce wannan yunkurin nasa wata sakayya ce ga Shugaba Trump ta amincewa da Tuddan Golan a matsayin yankin Isra'ila.

Isra'ila ta kwace Tuddan Golan daga Syria a 1967, inda a 1981 ta mayar da yankin a matsayin mallakarta duk da cewa a lokacin kasashen duniya ba su amince da wannan yunkurin ba.

Syria ta bayyana cewa matakin da Trump ya dauka cin fuska ne ga karfin ikonta.

A kwanakin baya ne Shugaba Netanyahu ya lashe zaben Isra'ila karo na biyar, inda a yanzu shugaban ya tafi yankin Tuddan Golan tare da iyalensa domin hutawa.

A inaTuddan Golan suke?

Yankin Tuddan Golan na da nisan kilomita 60 daga kudu maso yammacin Damascus babban birnin Syria.

Isra'ila ta kwace akasarin yankunan da ke Tuddan Golan a Syria a shekarar 1967 lokacin yakin Gabas Ta Tsakiya.

Tun a baya, Syria ta yi ikirarin cewa ba za ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila ba har sai ta janye dakarunta daga daukacin yankin na Tuddan Golan.

Akwai yankuna sama da 30 a Tuddan Golan da ke dauke da mutum sama da 20,000.

Amma wadannan yankuna ne da ba a amince da su ba karkashin dokar kasa da kasa duk da cewa Isra'ila ta musunta hakan.

Labarai masu alaka