Kalli bidiyon nadin sarautar dan China a Kano

Kalli bidiyon nadin sarautar dan China a Kano

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya nada Mike Zhang a matsayin 'Wakilin 'Yan Chinan Kano' a fadarsa da ke birnin Kano.

Zhang dan kasuwa ne, wanda ya shafe shekara 17 yana gudanar da harkokinsa a birnin na Kano.

Shi ne dan kasar China na farko da aka bai wa mukamin sarauta a Arewacin Najeriya.

Shi ne mamallakin kamfanin ruwan roba na Maya da ke unguwar Sharada a birnin Kano.

Sarkin ya ce ya nada shi sarautar ne saboda "kokarinsa wajen habbaka" kasuwanci a Kano, kuma yana fatan nadin nasa zai kara karfafa masa gwiwa.