Kaduna: An sanya dokar hana fita a Kajuru

Gwamnan Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai Hakkin mallakar hoto @elrufai

Gwamnatin jihar Kaduna a arewa masu yammacin Najeriya ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa'a 24 a karamar hukumar Kajuru.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar Samuel Aruwan ya ce hakan ya biyo bayan wata matsalar tsaro da ta faru ne a garin Kasuwan Magani ranar Alhamis.

Ya ce an dauki wannan matakin ne bayan wani zama da majalisar tsaron jihar ta yi a ranar Juma'a.

Har ila yau ya ce an tura jami'an tsaro yankin kuma kura ta lafa, "an shawo kan matsalar."

Wata sanarwa da gwamnatin ta wallafa a shafinta na Twitter ta bayyana cewa dokar ta fara aiki ne nan take.

Sakon ya ce Mataimakin Gwamnan jihar Barnabas Yusuf Bala, ya ba da umarnin daukar tsauraran matakai wajen tabbatar da aiki da dokar.

Mataimakin gwamnan, wanda shi ne mukaddashin gwamnan jihar ya kuma yi kira ga jama'ar yankin su ba da hadin kai ga matakin domin maido da zaman lafiya a yankin.

Wasu bayanai da BBC ta samu daga wasu majiyoyin gwamnatin jihar sun tabbatar da cewa an dauki matakin ne domin hana bazuwar wani tashin hankali da aka fuskanta a yankin.

Wasu rahotannin kuma sun nuna cewa mutane sun jikkata sakamakon tashin hankalin, to sai dai babu tabbas ko an samu asarar rai.

Me ke janyo tashin hankalin?

Yankin na Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru ya jima yana fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini.

Rikicin da yankin ke fama da shi dai ya ki ci - ya ki cinyewa ne sakamakon hare-haren ramuwar gayya da manyan kabilun da ke zaune a yankin ke kai wa juna.

Akwai dai zaman doya da manja da rashin yarda da ake yi tsakanin manyan kabilun yankin na Adara da Fulani.

Kowace kabila na zargin 'yar uwarta da kai mata hare-hare, abin da ke haifar da ramuwar gayya.

Ko a farkon watan Afrilun bana, gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya roki jama'ar yankin da su daina kai wa juna harin ramuwar gayya, saboda a cewarsa hakan ne ke rura wutar rikicin.

Tashin hankalin da yankin ke fama da shi ya tilasta wa wasu mazauna kauracewa gidajensu, inda suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira.

Gwamnatin jihar ta ce tana yunkurin magance matsalar tsaron, kuma tana aiki tukuru domin kare rayuka da dukiyoyi ta yadda kowa zai zauna cikin gidansa lafiya.

Labarai masu alaka