Abubuwan da ba ku sani ba kan Afirka, 'yanci da tsaro

'Yan Ethiopia Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Ethiopia a lokacin wani gangamin bayan hawa mulkin Firaminista Abiy Ahmed

'Yan Afirka a shirye suke su sadaukar da 'yancinsu, su karade inda suke so su kuma fadi ra'ayinsu, kuma za su amince a sanya masu ido indai hakan shi ne zai tabbatar masu da tsaro, kamar yadda wani bincike na kungiyar Afrobarometer ya bayyana.

Ga wasu abubuwa biyar da binciken ya gano:

1.'Yan Afirka da dama a shirye suke su musanya'yancinsu da tsaro

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana ganin shingayen binciken kan hanya a matsayin tukuicin ba da tsaro

Kungiyar Afrobarometer da ke bincike kan ci gaban Afirka ta bada shawarar cewa zabi tsakanin 'yancin kai ko kuma tsaro wata hanya ce da gwamnati za ta bi wajen shawo kan mutane su amince da ka'idoji da aka gindaya masu da ka iya shafar 'yancin su.

Bincike ya nuna cewa mutane da dama a shirye suke su sadaukar da 'yanci ko musanya 'yanci domin neman tsira da kwanciyar hankali.

Akasarin wannan bincike ko mu ce kashi 62 cikin 100 na binciken ya nuna cewa a shirye mutane suke su amince da dokar hana fita, da kafa shingayen binciken kan tittuna domin wanzuwar zaman lafiya.

Wani bincike da aka yi kan Madagascar ya nuna cewa kusan kashi 83 cikin 100 na al'ummar kasar su na cewa ''idan su na fuskantar matsaloli ko barazanar tsaro, gwamnati ta sanya dokar hana fita da kuma shingayen bincike domin takaita zirga-zirgar mutane.

Amincewa da wannan dokoki a cewar masu bincike, watakila baya rasa nasaba na halin da kasar ke ciki ''na kokarin farfadowa daga rikicin siyasa da ya daidaita kasar''.

2. 'Yan Afirka kalilan ke iya bayyana ra'ayoyinsu

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba kasaifai 'yan Tanzania ke iya fitowa su tofa albarkacin bakinsu ba

A kusan dukkanin kasashe, binciken ya nuna cewa ana samun koma baya a alkaluman mutane da ke iya fitowa fili su bayyana ra'ayinsu ko abubuwan da suke tunani.

Kusan kashi 2 cikin 3 (68%) na mutane da aka yi wannan bincike akan su sun nuna cewa mutane na ''yawaita'' ko ''takatsatsan'' da kalaman da ke fito wa daga bakinsu wanda ya shafi siyasa.

Kasar da ake ciki ko kuma ake samun karuwar yanayi na takatsantsan ita ce Mali, binciken ya bayyana cewa kasar ta fada cikin rikici tun juyin-mulkin 2012 da kuma barazanar da take fuskanta daga masu ikirarin jihadi a arewacin kasar.

Binciken ya kuma tabo Zambia da Tanzania a matsayin kasashen da mutane da dama suka nuna ba su da 'yancin fitowa su bayyana ra'ayinsu ko abubuwan da suke tunani.

Wadanan kasashen biyu, masu binciken sun yi bayani cewa ana masu kallon kasashen da gwamnatocinsu ke masu mulkin kama karya.

3. Mutane da dama a Afirka a shirye suke su amince da tsarin bibiyar abubuwan da suke yi

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An tambaye mutane ko za su amince gwammnati take bibiyar zantutukarsu ta sakonnin da suke karba a wayoyin hannu

Kashi 43 cikin 100 na mutanen da aka yi nazari a kansu a shirye suke su amince gwamnati ta sanya ido a kan su saboda bukatu na tsaro.

Mali ta fita daban.

Kashi 75 cikin 100 na bincike da aka yi a Mali ya nuna cewa 'yan kasar sun abince gwamnati take bibiyar ko sa ido a zantuttukansu, misali ta wayoyin hannu, domin tabbatar da cewa mutane ba sa kitsa rikici.

Binciken ya shawarci cewa ''rikicin tsatsauran ra'ayi na da nasaba na karuwar bukatar neman 'yanci ga kowanne mutum da kuma 'yancin farar hula''.

4.'Yan Afirka kalilan ne suka damu da kasancewa cikin wata kungiya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu zanga-zanga a Sudan na neman 'yanci da mulkin farar hula

Binciken ya bayyana koma bayan da ake samu karara kan nuna goyon-baya ga ''yancin walwala''.

Wannan dama ce ta kafa ko kuma kasance cikin wata kungiya, ta na iya kasance ta 'yan kasuwa ko siyasa da dai sauran kungiyoyi ko na agaji.

Ko, muna iya cewa, bukatar ita ce ganin a kafa wata kungiyar masu fafutika, misali irin wadda aka kafa kuma ta yi tasiri wajen kifar da dadaddiyar gwamnatin Sudan da Algeria.

Kashi 61 cikin 100 na mutane da aka yi binciken a kansu su amince da bukatar ''Kafuwar ko kasance cikin wata kungiyar wadda gwamnati ta amince ko ba a amince da ita ba''.

Sai dai a Zimbabwe ana samun koma baya ta bangaren mutanen da ke goyon bayan 'yancin kasancewa cikin wata kungiya.

Tun lokacin da ya hau mulki a 2017, gwamnatin Shugaba Emmerson Mnangagwa ke amfani da karfi kan masu zanga-zanga, musamman a manyan biranen da mutane ke adawa da matakansa na tsuke bakin aljihu.

Koda ya ke, mutane a Zimbabwe, da makwabciyar kasar Afirka ta Kudu da Mozambique, ba su wani nuna goyon-bayansu ba ga tsarin sadaukar da 'yanci saboda tsaro kamar yadda ya ke a wasu kasashen.

5. Goyon-baya ga 'yancin addini ya rabu biyu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An tambayi mutane ko a bai wa gwamnati damar takaita 'yancinsu na addini

Akwai rabuwar kawunan tsakanin mutane kan 'yancin tofa albarkacin baki kan abin da ya shafi addini, kaso 49 cikin 100 na goyon-bayan cikakken 'yanci, yayin da kaso 47 cikin 100 ke goyon-bayan matakan gwamnati na taikaita 'yanci ga addini.

Mutanen da suka fi nuna goyon-baya ga 'yancin tofa albarkacin baki kan addini sun fito ne daga Tunisia da Mali.

Sama da kashi 70 cikin 100 na mutane da ke rayuwa a wadanan kasashe sun amince da batun da ake cewa ''gwamnati ta kasance ta na da 'yancin sanya ido da takaita abubuwa da ake cewa a wuraren ibada, musamman tsakanin malamai da ke wa'azi ko amfani da kalamai da ka kasance barazana ga tsaron al'umma''.

Bincike ya nuna cewa wannan ya shafi kasashen da musulmi suka fi yawa wadanda suka sha fuskantar hare-haren tsatsauran ra'ayi - wani misali shi ne na mutane da suka zabi tsaro kan 'yanci.

Karin bayanai kan wannan bincike

  • An gudanar da wannan bincike na Kungiyar Afrobarometer ne a kasashe 34 na duniya
  • An ji ra'ayoyin mutane 45,832 tsakanin Satumbar 2016 zuwa 2018
  • Masu binciken sun tattara ra'ayoyi a kasashe 20 cikin shekaru 10

Labarai masu alaka

Karin bayani