Hare-haren Sri Lanka: 'Akwai bacin rai a zukatan jama'a'

Relatives cry at the graveside during the funeral of a victim of the Easter Sunday Bombings at a local cemetery on April 24, 2019 in Colombo Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani mutum da ya sha da kyar a harin bam din da aka kai a Sri Lanka ya bayyana cewa harin da aka kai ya sa kasar ta shiga cikin dimuwa da jimami.

Kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana, akwai tsaiko da aka samu wajen bangaren tattara bayanan sirri a kasar kafin kai harin wanda ya yi sanadiyar kashe mutane sama da 350.

Philip Weeraratne daga Colombo ya shaidawa BBC cewa ''jama'ar kasar na cikin zullumi.''

''Amma a yanzu , jama'a na cikin tsananin fushi, mutanen kasar sun fara cewa an san da batun kai harin kuma aka kasa dakilewa.''

Mista Weeraratne na hanyarsa ta zuwa wani otel mai suna Cinnamon Grand a wannan lokacin inda bam din ya fashe.

Image caption Bennington Joseph, da matarsa Chandrika da kuma 'ya'yansu duka uku da aka kashe

'Yan gidan daya kaf sun rasa ransu

Masu kai harin sun kai hare-haren ne a ranar Lahadin da ake bikin Easter a garuruwan Colombo da Negombo da kuma Batticaloa.

A wurare da dama, iyalen gida gaba daya sun rasa ransu harda yara.

Bennington Joseph mai shekaru 33 ya rasa ransa a harin da aka kai a cocin St. Anthony tare da matarsa da yaransa uku.

Mahaifin Jospeh ya nuna hoton danshi tare da matarsa a gefensa da yaransa da kuma dan karamin dansu da zai cika shekara daya a ranar 5 ga watan Mayu.

Ya ce ''muna kokarin shirye-shiryen bikin murnar zagayowar haihuwar dan autan Joseph, amma abin takaicin shi ne mun rasa shi.''

''Abin takaicin shi ne an rasa 'yan gida daya baki daya.''

Jin dadi da rashin sani

A lokacin da Mista Weeraratne ya ji karar abin fashewa a otel din da ke Cinnamon, ya dauka wasan wuta ne.

''A lokacin da na ji karar abin fashewar na biyu, sai na ga hayaki na fitowa daga gefen inda otel din yake, a nan ne na san cewa bam ne ya fashe.''

Ya tsallake rijiya da baya tunda bam din bai tashi da shi ba amma lamarin ya shafi abokansa.

Weeraratne ya rasa abokin kasuwancinsa wanda ya ke hutun Easter a otel din Shangri-la hotel.

A wannan otel din dai, wani abokinsa na kusa ya rasa matarsa da surukarsa a daidai lokacin da suke kokarin cin abincin safe.

''A nan ana maganar iyalai ne da suka je cin abinci a tare amma sun mutu.''

''Abin mamaki shi ne mintoci kadan kafin matar abokina ta mutu a harin bam din ta wallafa hotunansu a zaune da sauran jama'ar gida ana shirin fara cin abinci.''

Mutane sun shiga mamaki

Cikin sa'o'i kadan, irin zubar da jinin da aka yi a kasar ya fito zahiri wanda hakan ya yi sanadiyar mutane suka ci gaba da zama cikin gidajensu sakamakon tsoron da suke yi na kada a kara samun wani tashin bam din.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kammala yakin basasar kasar a watan Mayun 2009

Duk da cewa Mista Weeraratne wanda ke da shekaru 49 ya rasa abokansa a lokacin yakin basasar Sri Lanka, harin ya girgiza shi kwarai dagaske.

''A lokacin yakin basasar wanda ya faru fiye da shekaru goma da suka gabata, jama'a sun san cewa yakamata su zama cikin tsammani,'' kamar yadda ya bayyana.

'' Wannan lokacin ya saba da irin wancan lokacin da jama'a za su fito domin taimako wajen kawo abinci da magunguna da kudi, amma a yanzu jama'a na cikin fargaba kuma ba su da tabbacin abinda zai iya faruwa nan gaba.''

''Jama'a na cikin zullumi, ba su da karfin fita domin su taimakawa wadanda abin ya rutsa da su.''

Firai ministan kasar Ranil Wickremesinghe ya bayyana cewa mai yiuwa ne cewa kungiyar Isis na da alaka da hare-haren.

Nuna bacin rai ga jami'an tsaro.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Mista Weeraratne ya bayyana cewa jama'a sun nuna baccin ransu bayan da aka gano cewa gwamnatin kasar na da bayanan sirri da za su iya amfani domin dakile hare-haren.

A ranar 11 ga watan Afrilu, shugaban jami'an 'yan sandan kasar ya bayyana cewa akwai wata kungiya mai tsatsauran ra'ayi mai suna National Thowheth Jama'ath da ke da niyyar kai harin kunar bakin wake ga manya-manyan coci-coci inda ya bayyana cewa an samu bayanan sirrin ne daga wata sananniyar kungiyar leken asiri ta duniya.

An dai bayar da wannan bayanan ga manyan jami'an gwamnatin kasar amma firai ministan kasar da kuma mataimakin ministan tsaron kasar basu samu wannan bayanin ba.

Kusan kashi bakwai cikin 100 na mutane miliyan 20 na Sri Lanka mabiya addinin Kirista ne.

Mista Weeraratne ya bayyana cewa ''fushin 'yan kasar na zuwa kai tsaye ga jami'an gwamnatin kasar ba wai al'ummar Musulman kasar ba.''

Amma ya yi gargadi ga jami'an tsaron kasar inda ya bayyana cewa '' yakamata jami'an tsaron kasar su dauki mataki kada fushin wadanda abin ya shafa ya koma ga Musulman kasar da basu ji ba kuma basu gani ba.''

Labarai masu alaka