'Yan sanda sun mutu yayin sace ma'aikatan mai

View of Shell's oil and gas terminal on Bonny Island in southern Nigeria's Niger Delta taken 18 May 2005. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shell na aikin hakar man fetur da sarrafa iskar gas a yankin Neja Delta

'Yan sandan sun tabbatar da sace wasu manyan ma'aikatan babban kamfanin hakar man fetur biyu tare da kashe 'yan sandan da ke tsaronsu a yankin Neja-Delta mai fama da rikici a Najeriya.

Harin ya faru ne lokacin da ma'aikatan ke dawowa daga wata tafiya ranar Alhamis a kan titi cikin jihar Ribas.

'Yan bindigar sun kashe jami'an tsaro, a cikinsu har da matukin motar, kafin su kama ma'aikatan na kamfanin Shell.

Mai magana da yawun 'yan sanda na cewa ana kokarin ceto ma'aikatan da aka sace.

Ba a dai bayyana sunaye da kasashen da suka fito ba.

Wani mai magana da yawunsa ya ce: "Kamfanin Aikin Man fetur na Shell a Nijeriya (SPDC) na nadamar tabbatar da harin da aka kai kan ma'aikatansa da kuma jam'an tsaron gwamnati a Rumuji, jihar Ribas, a kan titin East/West".

Ma'aikatan na dawo ne daga wata tafiya da suka yi zuwa jihar Bayelsa.

Satar mutane don neman fansa, abu ne ruwan dare a Najeriya inda ake hakon turawa 'yan kasashen waje da ma sauran 'yan Najeriya, a baya-bayan nan har da mutanen karkara.

A farkon wannan wata ma, Wasu 'yan bindiga sun kashe wata 'Yar Burtaniya bayan sun je wani wurin shakatawa a cikin jihar Kaduna. An kuma sace karin mutum uku yayin harin ban da wadanda aka kashe.

Labarai masu alaka