Tattaunawa da dan wasan kwallon kafar Najeriya Odemwingie
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ina sha'awar shiga siyasa- Odemwingie

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon tattaunawar BBC da Osaze Peter Odemwingie

Shahararren dan wasan kwallon kafa na Najeriya wanda ya yi ritaya a kwanakin baya Osaze Peter Odemwingie, ya bayyana sha'awarsa ta shiga siyasa.

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawarsa da shashen Hausa na BBC.

Odemwingie ya ce yana so ya shiga siyasa saboda tana da tasiri ga yadda rayuwa ke gudana.

A hirar, an tambaye shi ko 'yan uwa da abokai na matsa masa da neman taimako?

Ya dai bayyana cewa wannan ba wani abu bane kuma ba nauyi bane a gareshi inda ya nuna cewa ba wani abu bane don ya taimaka wa 'yan uwansa.

Labarai masu alaka