Shin fashin karin-kumallo na kisa?

Kwai da burodi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Binciken ya nazarci dabi'ar karin-kumallon Amurkawa fiye da 6000

Akasari a kan bayyana karin-kumallo a mastayin mafi muhimmancin abincin da ya kamata a ci a kowace rana.

Wani bincike da kwalejin da ke nazarin cututtuka zuciya a Amurka wanda aka wallafa a watan Afrilu, ya ce tsallake cin abinci da safe na iya haddasa cututtukan zuciya masu janyo mutum ya rasa ransa.

Tawagar wasu likitoci da masu bincike daga jami'o'i da dama a Amurka ne suka gudanar da binciken.

Tawagar ta nazaraci mutane 6,550 da shekarunsu ya suka fara daga 40 zuwa 75 da ke kan wani tsarin kiwon lafiya tsakanin 1988 da 1994.

Mutanen da aka gudanar da binciken akansu sun bayanna sau nawa su ke karin-kumallo.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Binciken ya nuna cewa wadanda ke tsallake cin abincin safe sun fi yiwuwar kamuwa da cututtukan zuciya da zai iya zama ajalinsu

Kashi biyar cikin 100 na wadanda aka yi nazari akansu sun bayyana cewa ba su taba karin-kumalo ba, kashi 11 kuma sun ce da kyar suke yi, su kuma kashi 25 sun ce suna ci amma ba sosai ba.

Masu binciken sun kuma duba adadin wadanda suka rasa ransu zuwa shekara ta 2011 - mutum 2,318 cikin wadanda suka shiga shirin sun mutu - sai suka duba yawan cin abincin safe su.

Bayan da suka duba ko mutuwar ta su na da alaka da shan taba ko kuma kiba, sai tawagar ta gano cewa kashi 19 cikin 100 sun mutu sakamakon wasu dalilai, kashi 87 kuma sun mutu sakamakon cututtukan zuciya.

Gargadi

Binciken lafiya ya bayyana cewa tsallake karin-kumallo na iya yin mumunan illa ga lafiyar jiki, sai dai masanan kimiyya har yanzu na kokarin gano alakar wadanan abubuwa biyu.

A wani tsokaci da ta yi kan binciken, ma'aikatar lafiya ta Birtaniya ta wallafa wasu kalamai cewa jaridar ta Amurka ''ba za ta iya tabbatar da cewa rashin karin-kumallo ne ke saka cututtukan zuciya.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Binciken bai binciko yanayin cin abincin su gaba-daya a rana ba - kuma bai tabo mai suka fahimta da cin abincin safe ba

''Yawancin mutanen da binciken ya gano cewa ba sa karin-kumalo sun taba shan taba, ko giya ko ba su cika motsa jiki ba ko kuma ba sa cin abinci mai kyau."

"Kuma yawancinsu ba masu wadata bane,'' a cewar wata makalar da aka wallafa a shafin intanet na NHS, mai bayanan abubuwan da ke sa mutane su iya kamuwa da cututtukan zuciya.

''Binciken ya sanya ido ne kawai kan cin abincin safe sau daya, wanda hakan ba zai nuna dabi'o'in rayuwar mutum ba. Bai kuma binciki mai mutane suka fahimta da cin abinci ba.''

''Misali, yawancin mutane suna karin-kumallo kullum, amma za a iya samun bambanci tsakanin mutane masu cin abincin kirki da safe da kuma wadanda ke cin burodi ko kuma cakulat da hatsi''

Duk da haka, Dokta Wei Bao, wani farfesa a fanin lafiya da ke jami'ar Iowa kuma marubucin binciken ya kare abubuwan da ya binciko.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu binciken sun yarda cewa akwai alaka tsakanin cin abincin safe da kuma kamuwa da cututtukan zuciya

''Yawancin binciken da ake yi sun nuna cewa tsallake cin abincin safe na da alaka da kamuwa da ciwon suga, da hawan jini da kuma kitse,'' a cewar Bao.

''Binciken ya kiyasta cewa cin abincin safe zai iya taimakawa lafiyar zuciyar mutum.''

Babban mai kisa

Bao da abokanan aikinsa sun kuma rubuta cewa akwai alakar da ke tsakanin yawan cin abincin safe da kuma cututtukan zuciya ''an gano cewa ba su da alaka da wadatar mutum ko kuma jikinsa''.

''A tunaninmu, wannan shi ne bincike na farko kan alakar cin abincin safe da kuma cututtukan zuciya,'' inji masu binciken.

Cututtukan zuciya - musamman bugun zuciya da kuma shanyewar barin jiki - su ne manyan cututtukan da su ka haddasa mutuwar kashi 15 cikin 100 na mutane a 2016, a cewar hukumar lafiya ta duniya, WHO.

DO NOT DELETE OR TRANSLATE! Digihub tracker for [48051576]

Labarai masu alaka