Sarki Akihito: Sarkin Japan zai ajiye sarautarsa saboda tsufa

Japan's Emperor Akihito (L) and Empress Michiko (R) wave to well-wishers, APril 18 2019 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarki Akihito ne zai kasance sarki na farko da zai ajiye mukaminsa tun shekarar 1817

Sarki Akihito na kasar Japan ya kammala shirin sauka daga sarautar kasar domin dansa ya gaje shi.

Sarkin zai zama mai sarauta na farko da yayi haka a sama da shekaru 200 a Japan.

Sarki Akihito na da shekara 85 da haihuwa, kuma ya dauki wannan matakin ne bayan da tsarin mulkin kasar ya amine masa da yin haka saboda yana ganin tsufa da rashin lafiya sun hana shi sauke nauyin da ya rataya a kansa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yarima Naruhito mai shekara 59 da haihuwa ne zai gaji mahaifinsa

Bayan kwana daya da saukarsa, dansa Naruhito zai dare gadon sarautar Chrysanthemum wanda zai bude wani sabon babi a tarihin wannan dadadiyar kasar da ke yankin Asiya.

A Japan, sarki ba shi da wani iko na mulki amma wata alama ce ta hadin kan kasar.

A tsawon lokacin da ya ke rike da sarautar, Sarki Akihito ya zama abin so ga al'ummarsa saboda yadda ya rika kulawa da masu fama da cututtuka da matsalolin rayuwa kamar girgizar kasa da amabaliyar ruwa.

Yarima Naruhito da Gimbiya Aiko

Sabon sarkin zai kasance sarki na 126 a jerin sarakunan Japan.

Shekarunsa 59 da haihuwa, kuma ya halarci jami'ar Oxford ta Ingila kafin ya zama yarima mai jiran gado tun yana da shekara 28 da haihuwa.

A shekarar 1986 ya hadu da matarsa Gimbiya Masako Owada, kuma sun yi aure a 1993.

Suna da 'ya daya tilo mai suna Gimbiya Aiko, wadda aka haife ta a 2001.

Amma dokar kasar Japan ta haramtawa 'ya mace gadon sarautar kasar, saboda haka ba za ta gaji mahaifinta ba kenan.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gimbiya Aiko, 'ya daya tilo ta Yarima Naruhito

Kawun Gimbiya Aiko ne Yarima mai jiran gado na farko, sai kuma dan sa Yarima Hisahito wanda yaro ne mai shekara 12 da haihuwa.

Yadda gidan sarautar Japan ya kasance daga 1901 zuwa yau. Maza ne kawai ke iya gadon sarauta, kuma ana fargabar zuwan ranar da babu namijin da zai gaji sarautar.

Bikin sauka daga sarauta

Abu na farko da sarki Akihito yayi cikin shirin sauka daga sarautar shi ne na ziyarta wurin bauta na addinin Shinto, inda ya sanar da wadanda suka gabace shi a fagen sarauta cewwa ya yanke shawarar sauka daga mukamin.

Za a fara kuma a kamala bikin ne a yau Talata, kuma wannan ne karon farko da duniya za ta fara ganin yadda Sarki a Japan ke sauka daga mukaminsa.

A ranar laraba kuma, Yarima mai jiran gado Naruhito zai gaji sarautar, inda ake sa ran zai gudanar da aikinsa na farko a matsayin sabon sarkin japan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane masu yawa sun yi wa Fadar Sarki Akihito tsinke duk da ruwan sama mai yawa da ake yi