An yi jana'izar mutum 14 a Katsina

Katsina Hakkin mallakar hoto Honorabul Abduljalal Haruna Runka
Image caption An yi wa mamatan jana'izar ne a kauyen Gobirawa ranar Laraba

An yi jana'izar mutum 14, wadanda suka mutu sanadiyyar wani harin da wasu mahara suka kai karamar hukumar Safana ta jihar Katsina ranar Talata.

Dan majalisar dokokin yankin a majalisar jihar Katsina, Honorabul Abduljalal Haruna Runka, ya shaida wa BBC cewa maharan sun kai farmaki ne a kauyen Gobirawa da kuma Shaka Fito.

Ya ce: " 'yan bindigar sun kashe mutum 11 a Gobirawa, sai wasu guda uku da aka kashe a kauyen Shaka Fito. Akwai kuma wasu da suka jikkata."

"Masu satar mutane ne suka kai harin gab da sallar magriba, an turo jami'an tsaro, inda suka yi ba-ta-kashi da maharan," in ji shi.

Ya ce yawancin mutanen da suka mutu an kashe su ne a cikin gonaki saboda 'yan bindigar sun fara firgita garin ne, abin da ya sa mutane kowa ya yi ta kansa.

Hakkin mallakar hoto Honorabul Abduljalal Haruna Runka
Image caption An yi jana'izar wadanda suka rasun kamar yadda addinin Musulunci ya tanada

Ya kara da cewa an kashe wasu daga cikin maharan, wadanda galibinsu sun zo a kan babura. "Amma 'yan bindigar sun kwashe gawawwakinsu sun tafi da su," in ji shi.

Kazalika dan majalisar ya ce maharan sun sace mata da wasu daga yankin karamar hukumar.

Mai magana yawun rundunar 'yan sanda a jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya tabbatarwa da BBC harin.

Ya kuma ce rundanar 'yan sanda ta tura da karin jami'ansu bayan faruwar harin.

A farkon watan Afrilu ne jama'a daga yankunan kananan hukumomin da ke makwabtaka da dajin Kamako suka yi wani gangamin sa-kai suka shiga dajin domin kai wa maharan da ke addabar yankunansu samame.

Hakkin mallakar hoto Honorabul Abduljalal Haruna Runka
Image caption Tuni mutane suka fara daukar matakan kare kansu daga hara-haren 'yan bindigar

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa, mutane akalla 500 daga kananan hukumomin Katsina da ma wasu a Kaduna suka yi wannan gangami, inda suka shiga dajin.

Labarai masu alaka