'Yan bindiga sun kai hari 'makarantar mata' a Zamfara.

A woman in the Nigerian special forces Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rundunar sojin kasar ta kai dakaru don shawo kan lamarin

Wasu 'Yan bindiga masu satar mutane sun kai hari a wata makarantar sakandare ta Mata a jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da mata kuma wasu kananan yara suka bace.

'Yan bindigar sun kai harin ne a makarantar sakandare ta mata a garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi da dare, kamar yadda rundunar 'yan sanda a jihar ta shaida wa BBC.

SP Muhammad Shehu shi ne mai magana da yawun rundunar a jihar kuma ya ce mutum biyar ne suka bata a harin.

Cikinsu akwai kanan yara 3 da kuma mata biyu, wadanda masu dafa abinci ne a makarantar.

Mai magana da yawun fadar gwamnatin jihar Ibrahim Dosara ya ce ana ci gaba da neman wadanda suka bata.

Ya kuma kara da cewa daliban suna cikin koshin lafiya kuma babu wanda aka dauka daga cikinsu.

Sai dai wasu mazauna garin sun ce wadanda maharan suka dauka sun fi haka yawa.

Wata mata da ba ta so a bayyana sunanta ba ta ce mutum takwas ne aka dauke da farko, inda aka sako biyu daga cikinsu a ranar Alhamis.

Wani mazaunin garin shi ma ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun kashe mutum daya.

Ya ce 'yan bindigar sun bude wuta lokacin da suka shiga garin, inda suka kashe wani mutum guda.

Wani dan sa-kai a garin na Moriki ya ce tun da la'asar 'yan bindigar suka tare hanya kafin daga baya suka kawo hari da dare.

Ya ce sun tafi da wasu malamai biyu da wasu mata hudu masu dafa wa dalibai abinci, amma ba su yi nasarar isa inda daliban ke bacci ba.

Satar mutane don kudin fansa a Zamfara na ci gaba da karuwa a baya-bayan nan, duk da yunkurin jami'an tsaro na kawo karshen matsalar da ta addabi yankin arewa maso yammaci.

Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu, yayin da yara da dama suka kasance marayu sakamakon kashe-kashen da ke faruwa a jihar.

Labarai masu alaka