Za a biya sama da N7bn a matsayin diyyar rai

Australian woman Justine Damond

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Justine Damond

Hukumomin birnin Minneapolis a Amurka sun amince da biyan diyyar dala miliyan ashirin kwaankwacin naira biliyan bakwai da miliyan 200 ga dangin wata mata 'yar kasar Astireliya da wani dan sanda ya kashe ba tare da tana rike da wani makami ba a shekara ta 2017.

Mohamed Noor ya harbe Justine Ruszczyk Damond ne bayan ta kira 'yan sanda don ba da rahoton yiwuwar aikata cin zarafi.

Sai a watan Yuni za a yankewa dan sandan hukunci bayan kotu ta same shi da laifin aikata kisan kai ranar Talata.

'Yan'uwan marigayiyar sun ce za su ba da gudunmawar dala miliyan biyu kwatankwacin naira miliyan 700 don tallafawa masu yaki da harbe-harben bindiga.

Lauyansu ya ce baki alaikum suka nuna gamsuwa da wannan matsaya da aka cimma.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

An tsare Mohamed Noor bayan an same shi da laifi

Al'amarin nata ya harzuka rayukan mutane a kasar Astireliya da Amurka, inda 'yan sanda ke harbe kimanin mutum dubu guda a kowacce shekara.

Shari'ah ta saurari cewa matar wadda Ba'amurkiya ce 'yar asalin Astireliya ta kwanta shame-shame cikin jini sakamakon harbin bindiga minti guda bayan ta gama hira a wayar tarho da saurayinta.

Ta fada wa Don Damond cewa 'yan sanda sun iso bayan ta kira su don ba da rahoto kan yiwuwar aikata cin zarafi a wani layi da ke bayan gidansu.

Mohamed Noor ya fada wa kotu cewa ya tuna lokacin da ya ga wata mata mai jan gashi da riga ruwan hoda ta tunkaro motarsa a daren da harbin ya auku.

Ya ce ya yi imani barazana ce ta tunkaro bayan ya ji wani amo mai karfi kuma ya ga Misis Damond ta daga hannunta na dama.

Noor ya ce abokin aikinsa, Yallabai Matthew Harrity, cikin ihu ya ce "Oh Allah!" kuma hannunsa yana bari a lokacin da yake kokarin rarumar bindigarsa kafin "ya juyo gare ni cikin fargaba a idanunsa".

Wanda ake karar ya ce "kafin kiftawa da bismillah ya yanke shawara" inda ya harbe matar daga cikin tagar mota.