Ebola ta kashe mutum 1000 a Congo

Bullar cutar karo na biyu a Congo shi ne mafi muni a tarihi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bullar cutar karo na biyu a Congo shi ne mafi muni a tarihi

Yawan mutanen da suka mutu sakamakon sake bullar cutar Ebola sun kai mutum 1000 kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ta bayyana.

Wannan ne karo na biyu na sake barkewar cutar wanda ya faru a Augustan bara kuma wannan barkewar ita ce ma fi muni a halin yanzu.

Mataimakin Daraktan Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Dakta Michael Ryan ya bayyana cewa rashin yarda da jama'a ke nunawa ga ma'aikatan lafiya da kuma rashin zaman lafiya na cikin abubuwan da ke kawo tsaiko wajen dakile yaduwar cutar wanda a yanzu haka tana kara yaduwa zuwa gabashin kasar.

Mista Ryan ya shaida cewa sau 119 ana kai hare-hare ga cibiyoyi da ma'aikatan lafiya a kasar tun watan Junairu.

Ya bayyana cewa hukumar lafiyar ta yi hasashen cewa za a ci gaba da samun yaduwar cutar matuka a kasar Congo

Ma'aikatan lafiya a kasar sun bayyana cewa akwai rigakafin cutar da dama a kasar- tuni aka ba mutane dubu 100 magunguna. Amma ci gaba da samun rikici a gabashin kasar inda akwai 'yan tayar da kayar baya da kuma rashin yarda da likitoci na kara mayar da hannun agogo baya ta fuskar shawo kan matsalar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mista Ryan ya ce '' Har yanzu muna da matsala da al'ummomi wajen yarda da amincewa da mu.''

Baya ga cutar Ebola, Jamhuriyyar Dimokradiyar Congo na fama da barkewar cutar kyanda wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutum 1000 da kuma masu fama da cutar kusan 50,000.

Mece ce Ebola?

Ebola wata kwayar cutar virus ce wadda alamun kamuwa da ita na farko suka hada da zazzabi mai zafi da ya wuce kima da kasala mai karfi da ciwon gabobi da rikewar makogwaro a cewa Hukumar lafiya ta duniya.

Sai matakin cutar na gaba wato amai da gudawa da kuma a wasu lokuta, zubar jini a ciki da kuma jiki.

Cutar Ebola na yaduwa a tsakanin mutane ta hanyar ta'ammali da dabbobin da suka kamu da cutar irinsu gwaggon Biri da Jemage da Gada.

Daga nan sai ta yadu tsakanin mutane ta hanyar jini da danshin jiki ko na gabobin jiki ko kuma ta hanyar dauka daga muhallan da suka gurbata.

Hatta jana'izar gawar mai Ebola tana iya zama hatsari, idan masu makoki suka taba jikin mamacin.

Kwayoyin cutar kan dauki tsawon kwana biyu zuwa makonni uku kafin su kyankyashe, kuma kula da wadanda suka kamu da cutar abu ne mai wuya.

Ma'aikatan lafiya suna cikin hatsari idan suka duba lafiyar wanda ya kamu, ba tare da daukar matakan kariyan da suka dace ba.

Asalin Ebola

An fara gano cutar ne a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo cikin shekarar 1976 tun lokacin ne ta ci gaba da yaduwa a tsakanin kasashen gabashin Afirka ciki har da Uganda da Sudan.

Cutar tana da bazata don kuwa ta bulla a kasar Guinea a watan Fabairu, wadda ba ta taba saninta ba a baya, inda take ci gaba da yaduwa a birane.

A Najeriya, cutar ta bulla ne a 2014, bayan an killace wani mutum dan Liberia da ya je Lagos a cikin watan Yulin shekarar, kuma daga bisani Ebola ta yi sanadin mutuwarsa.

Tun daga nan ne daya daga cikin likitoci da ma'aikatan jinyar da suka kula da shi suka kamu, hukumomin kasar sun kuma tabbatar da mutuwar wata jami'ar a cikinsu, wadda ita ce 'yar Najeriya ta farko da ta mutu sakamakon cutar, ya yin da kuma aka kebe wasu mutane takwas a jihar Lagos, kuma biyar daga cikinsu an tabbatar suna dauke da cutar.