Yadda aka kirkiro kidan BBC Hausa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda aka kirkiro kidan BBC Hausa

Shin wane ne ya yi gogen nan da ake bude shirin rana da na yamma da shi a tashar rediyon BBC Hausa?

Wannan ita ce tambayar da wani tsohon ma'aikacinmu Muhammad Ibrahim (Makaman Ringim) ya amsa mana a shirinmu na Amsoshin Takardunku na wannan mako.

Ya ce wani mai goge wanda ake kiransa Lauri Katsina ne ya kirkire shi a lokacin Yakin Duniya na Biyu.

An fara amfani da shi ne tun lokacin da aka bude kafar yada labarai ta BBC Hausa a watan Maris din shekarar 1957.

Latsa alamar lasifika a jikin hoton da ke sama don sauraron cikakken karin bayanin da tsohon ma'aikacinnamu ya yi:

Labarai masu alaka