"Akwai wadanda suke neman mu domin su kashe mu" - Anas Aremeyaw Anas
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

"Duk da kashe Ahmed Suale ba za mu bar binciken kwakwaf ba” - Anas Aremeyaw Anas

Sashen Hausa na BBC ya samu tattaunawa da dan jarida mai binciken kwakwaf na kasar Ghana, Anas Aremeyaw Anas.

Dan jaridan shahararren ne a fannin aikin jarida na binciken kwakwaf ta hanyar daukar hoto ko bidiyo na masu aikata laifin cin hanci da rashawa a lokacin da suke yi.

Daga cikin bincikensa akwai; "Doctor Dra", na wani likitan da ke zubar wa da mata ciki amma yana kwana da su a kafin ya yi masu tiyata.

Bincikensa ya jawo kora da daure jami'an kasashe daban-daban a kan laifin aikata rashawa.

Hakkin mallakar hoto Anas Aremeyaw Anas
Image caption Irin salon binciken nasa ta hanyar amfani da kyamara a boye

A farkon shekarar 2019 ne aka harbe kashe abokin aikinsa Ahmed Hussain Suale ta hanyar harbinsa da bindiga.

A cewar Anas, "Ni da Ahmed Suale daman akwai wadanda suke neman mu su kashe mu, amma sai muka tsallake"

"Amma duk abin da Allah ya kaddarawa mutum ko da zai je sama ko kasa sai ya same shi" a cewar Anas din.

Hakkin mallakar hoto Anas Aremeyaw Anas
Image caption Ya kan yi amfani da salo iri ire domin kulle fuskarsa

Ya kuma sha alwashin cewa ba za su bari mutuwar Ahmed ta hana su binciken kwakwaf ba.

Hakkin mallakar hoto Anas Aremeyaw Anas
Image caption Wani zanen Anas da aka yi a bango domin gargadi ga masu aikata rashawa

"Su masu aikata abubuwan nan marassa kyau, burinsu shi ne idan suke kashe Ahmed sai mu bar aikin, amma ba za mu bari ba"

Ya kara da cewa "Ahmed dake a wajen Allah idan ya ga kamar mun bar aikin nan abin ba zai masa dadi ba"

Hakkin mallakar hoto Anas Aremeyaw Anas
Image caption wasu daga cikin hulunan dan jaridan

Anas kuma ya shaida mana cewa akwai wani aikin da suke yi a Najeriya mai suna 'Nigeria Investigates' domin su yi yaki da rashawa.

Ya bayyana cewa zai ci gaba da kulle fuskarsa domin su na yin hakan ne saboda tsaron rayukansu.

Hakkin mallakar hoto Anas Aremeyaw Anas
Image caption Aiki sai mai shi

Cikakkiyar hirara na a shafinmu na Youtube, www.youtube.com/user/bbchausa

Labarai masu alaka