Yayin da Zainab Aliyu ta yi arbi da 'yan uwanta a Kano
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An yi kukan farin ciki da dawowar Zainab Aliyu gida

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon da ke sama

Zainab Aliyu ta dawo gida Najeriya ne bayan ta shafe fiye da watanni hudu a tsare a wajen hukumomi Saudiyya.

Ta dawo kasar ne a safiyar Litinin 13 ga watan Mayu da misalin karfe 10:00 na safe inda ta sauka a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano (MAKIA) da ke birnin Kano.

Tun a watan Disambar bara ne dai jami'an tsaro a kasar Saudiyya suka kama Zainab Aliyu jim kadan bayan isarsu kasar domin yin aikin Umara ita da mahaifiyarta Maryam da kuma 'yar uwarta Hajara.

Jami'an tsaron sun zarge ta da safarar kwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta.

Sai dai daga baya da aka zurfafa bincike hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA ta gano cewa wasu ma'aikata ne a filin jirgin saman MAKIA suka saka mata kwayar a jakarta.

Kwamandan hukumar mai kula da MAKIA Ambrose Omorou ya tabbatar wa da BBC cewa tuni suka kama mutum shida, wadanda ake zargi da aikata hakan.

Uku daga cikinsu ma'aikata ne da ke tantance kayayyakin matafiya, daya ma'aikacin wani kamfanin sufurin jirgin sama ne, sauran biyun kuma jamai'an tsaro ne a filin jirgin saman.

Yadda aka sako Zainab

Tun bayan da aka gano cewa Zainab na da gaskiya game da zargin da ake yi mata, 'yan Najeriya mazauna kasar da ma wadanda suke zaune a kasashen ketare sun ta gudanar da zanga-zanga da kuma kiraye-kiraye musamman a shafukan sada zumunta domin ganin cewa gwamnatin Najeriya ta sa baki wajen sako Zainab.

Bayan haka ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Shari'a Abubakar Malami da ya shiga maganar Zainab Aliyu.

Najeriya ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wanda kwanaki kadan bayan umarnin shugaban kasar aka mika Zainab ga ofishin jakadancin Najeriya da ke Saudiyya.

Zanga-zangar da ta fi jan hankali ita ce zanga-zangar da daliban makarantar jami'ar Maitama Sule da ke Kano suka gudanar inda jami'ar ce Zainab ke karatu kafin tsare ta.

Kungiyoyin kare hakki kamar su Amnesty International da sauran kungiyoyin kare hakkin bil adama da kuma masu fada a ji a shafukan sada zumunta da malaman addini sun taka muhimmiyar rawa wajen gwagwarmaya domin kwato hakkin Zainab.

Labarai masu alaka