Shin da gaske Yusuf Buhari ya mallaki biliyoyin daloli?

Yusuf Buhari Hakkin mallakar hoto Facebook

An rika yada wani labari da ake dangantawa da mujallar Forbes inda aka ruwaito Yusuf Buhari, wato dan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayi na hudu a jadawalin 'ya'yan shugabannin kasashen duniya da suka fi kudi a fadin duniya.

Rahoton ya yi ikirarin cewa Yusuf Buhari ya "mallaki dala biliyan 2.3."

Mutane musamman a kafafen sada zumunta sun rika yada wannan labari a shafukan Facebook da Twitter kuma labari ya samo asali ne daga wasu kafafen yada labarai a Najeriya.

Mene ne gaskiyar wannan ikirarin?

Binciken da kafar yada labarai ta AFP ta yi ya gano cewa labarin bogi ne saboda mujallar Forbes ba ta wallafa wani rahoto da ke cewa Yusuf Buhari ya mallaki dala biliyan 2.3.

Mu ma bincikenmu ya nuna cewa babu kanshin gaskiya a wannan labarin don babu wata babbar kafa mai sahihanci da ta wallafa wannan labarin.

Mujallar Forbes ta wallafa jerin sunayen manyan attajiran Afirka na 2019 kuma 'yan Najeriya hudu ne kawai suka shiga jerin. Amma babu Yusuf Buhari a cikinsu.

Wato Alhaji Aliko Dangote wanda ya mallaki dala biliyan 10.3, sai Mike Adenuga wanda ya ke matsayi na biyu kuma ya mallaki dala biliyan 9.2.

Abdulsamad Rabiu (mai kamfanin siminti na BUA) yana matsayi na uku inda ya mallaki dala biliyan 1.6.

Yadda ake gane labaran karya

Akwai yiwuwar ci gaba da samun labaran karya musamman a lokutan zabuka.

Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana'ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da dama aka kashe a rikicin manoma da makiyaya wanda aka ce labaran karya na kara zuzutawa

Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa.

Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.

Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu.

Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?

Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa.

Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.

Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na'urar da aka yi amfani da ita.

Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.

Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani.

Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu yake.