An rufe shafukan sada zumunta saboda satar amsar jarrabawa

Student writing exam
Bayanan hoto,

Sama da dalibai 31,000 ne dage jarrabawar ya shafa

Somaliya ta daga jarrabawar makarantun sakandare bayan da suka gano cewa an yi ta yada tambayoyin da za su fito a shafukan sada zumunta tamkar wutar daji.

Ministan Ilimi Abdullahi Godah Barre ya ce an soke duk wata jarrabawa da aka riga aka yi.

Soke jarrabawar da aka yi ya jawo zanga-zanga a Mogadishu, babban birnin kasar.

A yanzu dai za a yi jarrabawar ne cikin kwana biyar a karshen watan Mayu, kuma za a rufe shafukan sada zumunta saboda gudun bayyanar tambayoyin da za su fita.

Har yanzu dai ba a san matakan da za a bi wajen rufe shafukan ba, kuma ko abun zai shafi kaar ne baki daya.

Mr Barre bai kuma fadi ko tun farko ana amfani da kafofin sada zumunta ba wajen sanya takardun jarrabawar.

An yi ta sayar da takardun jarrabawar kuma wata kungiyar bata gari ta yi ta yada su a shafukan sada zumunta, a cewar wani gidan rediyo na kasar Dalsan.

Tun ranar Asabar ne dalibai suka fara zana jarrabawar kammala sakandare kuma ya kamata su kammala cikin mako daya, amma Mista Barre ya ce dagawar ya zama wajibi.

"Abun takaici ne mai satar amsa ya zauna aji daya da dalibi mai kwazo. Don haka ma'aikatar ilimi ta dauki matakin soke jarrabawar da aka riga aka yi da ma fasa yin wacce ta rage," kamar yadda ya fada yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin.

Fiye da dalibai 31,000 ne daga jihohi daban-daban na Somaliya dage jarrabawar zai shafa.

An yi ta yada wa wani bidiyo na Mista Barre da shugaban 'yan sanda a intanet suna kwantar wa da daliban hankali, wadanda suke ta zanga-zanga saboda dage jarrabawar.