Kano: Masu zaben sarki sun gurfanar da Ganduje da majalisa a gaban kotu

Masarautar Kano Hakkin mallakar hoto Getty Images

Madakin Kano da makaman Kano da Sarkin dawaki mai tuta da Sarkin ban Kano, sun shigar da kara gaban babbar kotun jihar suna kalubalantar kafa wasu sababbin masarautu a jihar.

Wadanda manyan hakiman suka kai kara sun hada da shugaban majalisar dokokin jihar Kano da majalisar da gwamnan jihar Kano da kwamishinan shari'a na jihar da Sarkin Rano da na Karaye da na Gaya da kuma na Bichi.

Suna neman kotun ne ta soke masarautun, wadanda majalisa da gwamnatin jihar suka kirkiro a watan Mayu na 2019, sannan a hana sarakunan gudanar da duk wani aiki da sunan sarakuna masu daraja ta daya.

Lauyoyi 24 ne suka shigar da karar a madadin hakiman, cikinsu kuwa har da manyan lauyoyi masu darajar SAN su bakwai.

Manyan hakiman hudu da suka shigar da karar su ne na gaba-gaba a majalisar sarkin Kano, sannan su ne suke zabar sarki gabanin nada shi.

A shekarun 1980 ma masu zaben sarkin sun shigar da irin wannan kara bayan da gwamnatin lokacin da jam'iyyar PRP karkashin Muhammadu Abubakar Rimi ta kirkiro karin masarautu a Kano a lokacin Sarki Ado Bayero.

Sai dai a lokacin, gabanin yanke hukunci sai sabon gwamnan jihar Sabo Bakin Zuwo ya rushe masarautun.

A tsarin kirkirar sababbin masarautun dai, duka masu zabar sarkin za su daina aiki a masarautar Kano, inda Madaki da Sarkin Bai suka koma karkashin sabuwar masarautar Bichi, yayin da makama da sarkin dawaki mai tuta kuma suka koma karkashin masarautar Gaya.

Dukkansu sun nuna rashin amincewa da wannan tsari, inda suka ce hakan zai raba su da aikin da suka gada sama da shekara 200, wato tun lokacin da Fulani suka ci Kano a lokacin jihadin Shehu Dan Fodiyo.

Sannan sun yi zargin cewa yanayin da aka yi dokar cikin kwanaki kalilan na nuni da irin mummunar manufar da ake da ita na lalata tarihin masarautar na fiye da shekara 2000, ta hanyar kirkirar masarautun Bichi da Gaya da Karaye da kuma Rano.

Takardar karar ta ce an yi karan tsaye ga dokar kananan hukumomin ta 1984 wadda ta bayyana yadda za a kare tarihi da kuma aikin masu zaben sarki.

Har ila yau sun bayyana cewa akwai tufka da warwara a cikin dokar da kuma tsagwaron karya, inda ta ce za a yi masarautu hudu ne amma sai ga shi sun koma biyar.

Abinda masu kara ke bukata

Masu zabar sarkin sun bukaci kotun ta dakatar da dokar kirkirar masarautun wacce majalisar dokokin jihar ta yi, Gwamna Ganduje kuma ya sanya mata hannu, sannan sun bukaci kotun ta hana gwamnan Kano mika wa sababbin sarakunan takardun kama aiki da sandar girma.

Masu karar sun ce idan kuma har an ba su sandar da takarda sun nemi kotun ta soke matakin.

Sannan ta nemi kotun ta hana sababbin sarakunan gabartar da kansu a matsayin sarakunan Rano da Karaye da Gaya da kuma Bichi.

Sannan kuma ta hana sarakunan Rano da Karaye da Bichi da kuma Gaya kiran kawunan su a matsayin sarakuna ko kuma wani ya kira su da hakan.

Sannan ta dakatar da gwamnan Kano da yin dukkan wani yunkuri na kwace karfin ikon da ke hannun masu zaben sarkin Kano, ko kuma amfani da wani karfin iko wajen cire su ko mayar da su wasu wuraren sabanin inda suke yanzu.

Har ila yau, sun bukaci kotun ta hana gwamnan Kano sauke sarkin Kano ko sauya masa masarauta ba tare da an shawarci ko tuntubar masu zaben sarki ba.

Wannan karar na zuwa ne a daidai lokacin da wata babbar kotun jihar da ke Ungogo za ta fara sauraron karar da wasu 'yan majalisar dokokin jihar suka shigar, suna kalubalantar hanyoyin da aka bi wajen samar da dokar, abin da suka ce an saba ka'idojin zaman majalisar.

Labarai masu alaka