Ba mu gaza ba wajen yaki da masu satar mutane – Dambazau

Dambazau Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Dambazau ya ce gwamnati na aiki tukuru da taimakon wasu shugabanni don ganin an kawo karshen satar mutane

Gwamnatin Najeriya ta ce ana samun nasara a yaki da migayun ayyukan da ake aikatawa a kasar musamman satar mutane don neman kudin fansa.

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ne ya shaida haka a yini na biyu na taron shugabannin rundunonin 'yan-sanda na kasashen yammacin Afirka da ake yi a Abuja.

Ya ce "gwamnatin tana aiki tukuru da hadin-kan wasu shugabanni wajen ganin ta shawo kan matsalolin tsaro musamman garkuwa da mutane domin neman kudin fansa'.

Manufar taron wanda ya samu halartar jami'an hukumar 'yan sandan kasa da kasa ita ce duba kalubalan tsaro da yankin ke fuskanta da kuma yadda masu aikata laifi ke ketara iyakokin kasashen.

Janar Dambazau ya ce a baya ba a san matsalar satar mutane ba, amma dai a halin yanzu an dukufa ana tuntubar juna da wasu shugabannin daban-daban na yankuna don gani an kawo saukin wannan al'amari.

Mutane da dama dai na ganin akwai gazawar gwamnati la'akari da yadda matsalar garkuwa da mutane ke neman zama ruwa dare a sassana arewacin Najeriya.

Sai dai Janar Dambazau ya ce "ba wai an gaza ba ne ta wani fannin kawai dai ba rana guda ake gano bakin zaren ire-iren wadanan matsalolin ba.

Ya kuma ce yanzu idan aka kwatanta da baya kusan ana iya cewa an samu "saukin" matsalar tsaro musamman a kan titin Kaduna zuwa Abuja.

Har ila yau ya kuma ce an kama mutane da dama da ke cikin wannan harka ta satar mutane a yankunan da dama kamar su Zamfara da sauransu.

Kasashe irinsu Najeriya da Nijar da Mali da Burkina-Faso na daga cikin kasashen da matsalar ta'addanci da masu tayar da kayar baya ta fi addaba.

Image caption Jihar Zamfara na daya daga cikin yankunan da ke fuskantar satar mutane

Haka nan kuma akwai matsalar masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma fataucin bil-Adama da yaduwar miyagun makamai tsakanin farar hula da dai sauransu.

Manufar taron wanda ya samu halartar jami'an hukumar 'yan sandan kasa da kasa ita ce duba kalubalan tsaro da yankin ke fuskanta da kuma yadda masu aikata laifi ke ketara iyakokin kasashen.

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya ya ce za su yi amfani da wannan dama wajen gani an kakkabe duk mutane da ke neman zamewa kasar alakakai.

Labarai masu alaka