Zimbabwe ta sayar wa China giwaye 93

Giwa Hakkin mallakar hoto AFP

Zimbabwe ta samu dala miliyan 2.7 wajen fitar da giwaye 97 zuwa China da Dubai a cikin shekaru shida, a cewar ministar yawon shakatawa Priscah Mupfumira, in ji jaridar Chronicle.

Ta ce dabbobin da aka fitar ba manya ba ne ba, kenan ana nufin ba su wuce shekara biyu ko uku ba.

Hukumar da ke kula da gandun daji ta Zimbabwe ta fitar da a kalla matasan giwaye 97 zuwa China da Dubai tsakanin 2012 da kuma daya ga watan Janairu na 2018.

"An fitar da a kalla giwaye 93 zuwa China da wasu hudu kuma zuwa Dubai," in ji ministar.

An siyar da giwayen kan kudi kimanin dala 13,500 zuwa 41,500, a cewar jaridar.

Ms Mupfumira ta ce kudaden da ake samu daga sayar da su za a yi amfani da su wajen gyara rayuwar giwaye.

''Iyakar giwayen da Zimbabwe za ta iya dauka 55,000 ne amma a yanzu muna da giwaye 85,000,'' in ji ta.

Ms Mupfumia ta ce ba za su iya rage giwayen ba saboda dokokin da kungiyar Cites mai kula da cinikayyar dabbobin da ke fuskantar barazanar bacewa ta sanya.

An tattauna lamarin a kwanakin baya a wani taron kolin da aka yi a garin Kasane da ke Botswana.

Tare da Namibia da kuma kasar Afrika ta Kudu, Zimbabwe na matsawa ta ga an daina farautar giwaye ba bisa ka'ida ba, kuma tana bukatar Cites ta goya mata baya domin barin a dinga sayar da giwaye saboda a samu kudaden da za a inganta rayuwar sauran giwayen.

''Muna da giwaye wadanda idan mun sayar da su za mu iya samun kusan dala miliyan 300, kudin da za mu iya amfani da su wajen shirye-shiryen inganta rayuwar giwaye tare da kuma amfanar da al'ummomin da suke rauyuwa kusa da gandun daji,'' a cewar Ms Mupfumira.

Labarai masu alaka