Kano: Shin gwamnoni na katsalandan a harkar masarautu a Najeriya?

Kano emirate - Masarautar Kano Hakkin mallakar hoto Patrick van Katwijk
Image caption Sarki Muhammadu Sanusi ya yi aiki a matsayin shugaban babban bankin Najeriya tsakanin 2009 zuwa 2014 kafin ya karbi sarautar

Labarin matakin da majalisar dokokin jihar Kano ta dauka na raba masarauta mafi girma a Najeriya, wato masarautar Kano zuwa kashi biyar ya janyo ce-ce ku-ce da dama daga 'yan kasar.

Wasu na cewa da gangan gwamnatin ke so ta yi haka domin karya karfin sarkin Kano na yanzu wato Muhammadu Sanusi na II, wanda mutane ke cewa yana yawan sukar gwamnatin jihar.

Sai dai gwamnatin ta musanta zargin.

Duk da cewar an kafa masarautar ta Kano tun a karni na 15 kuma ana danganta ta da batutuwan da suka shafi jihadi da yake-yake tun shekara ta 1903.

Kano dai ba ta taba gamuwa da rarabuwar masarauta ba. Sai dai akwai lokutan da ake samun sauyin sarki daga wannan gidan sarauta zuwa wani, bayan mutuwa ko yin murabus din sarki.

Kano na da kananan hukumomi 44 da kuma mutane kimanin miliyan tara, sai dai kirkirar sababbin masarutun da rage karfin ikon Sarkin Kano zai rage yawan kananan hukumomin da za su kasance karkashin sarkin Kano daga 44 zuwa 10, abin da mutane da dama ke tsoron zai iya wargaza tsari da kuma ikon masarautar ta Kano.

Bayan da aka aiwatar da wannan dokar, wacce majalisar da kuma gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje suka sanyawa hannu a ranar 8 ga watan Mayu, masarautar ta Kano wacce ta kai shekara 200 a karkashin mulkin gidan Fulani, na fuskantar wani sabon shafi a tarihinta.

Sabuwar dokar za ta tabbatar da cewar sarkin Kano na yanzu, Alhaji Muhammadu Sanusi na II, wanda yana daya daga cikin shugabannin addini da na gargajiya mafiya iko a arewacin Najeriya, zai tsira da kashi daya daga cikin biyar kawai na masarautarsa.

An kirkiro sababbin masarautu hudu kuma dukkanin su an mayar da sarakunansu masu daraja ta daya, yayin da ak nada sabon sarki a masarutar Bichi.

''Ko Turawan mulkin mallaka ba su yi kokarin wargaza tarihin Kano kamar yadda aka yi a yanzu ba,'' in ji Farfesa Tijjani Naniya, na sashen tarihi daga Jami'ar Bayero da ke Kano.

Ya ce kirkiro da sababbin masarautun da aka yi tamkar bata tarihi ne da bai kamata a bari ya faru ba.

Hakkin mallakar hoto ISSOUF SANOGO
Image caption Marigayi Sarki Ado Bayero dan uwan kakan sarki Muhammadu Sanusi na biyu ne

''Abin da ya faru a Kano a cikin makon da ya gabata tamkar kokarin sauya tarihin mutane ne, tarihin da ya fi shekara 1000, ko lokacin da Turawan mulkin mallaka suka zo ba su yi kokarin sauya tarihinmu ba, to me ya sa za a yi hakan yanzu?

"Yaya za a yi wasu mutane su wargaza tarihin da ya dade haka, duk a cikin kwana uku kuma ba tare da shawara da mutane ba, daga gani akwai wata manufa,'' in ji Farfesa Naniya.

Gwamnatin Kano dai na kallon lamarin ta wani bangare na daban. A cikin wata sanarwa, ta ce, ''an dauki matakin raba masarautun na Kano ne domin matso da bangaren gargajiya kusa da mutane.''

Farfesan ya kuma ce a ganinsa masarautun biyar maimakon guda daya ba za su dade ba, ko a shekara ta 1982 da tsohon gwamnan jihar Abubakar Rimi ya yi kokarin aikata hakan, bayan shekara daya maganar ta rushe.

''Gwamna Rimi ya kuma yi kokarin aikata hakan a 1982, kuma lokacin da tsohon gwamna Sabo Bakin Zuwo ya hau mulkin jihar, sai ya soke rarraba masarautun da gwamna Rimi ya yi saboda yawancin mutanen kano sun bayyana cewa bai dace ba kuma a lokacin sun ce tamkar ana kokarin wargaza tarihinsu ne.

"A yanzu ma ina sa ran hakan zai kara faruwa.''

Wani mazaunin Kano Zakari Mohammed ya ce duk da cewar za a wargaza tarihin jihar, amma an yi shi ta hanya mai kyau saboda a tunaninsa mutanen da ke karkashin sababbin masarautun za su fi jin an ja su a jiki.

''Na yarda cewa a wani bangaren an taba tarihin Kano amma ni a ganina kafa wadannan sabbin masarautun zai sa mutane su fi jin an ja su a jiki.

"Kafin yanzu sarakunan da ke karkashin wadannan sababbin masarautun suna dogara ne kan sarkin Kano domin jagoranci da kuma shawarwari, amma yanzu za su iya yin komai da nasu sarakunan wadanda ma suka fi kusanci da su.''

Shi ma Abdullahi Sani wani mazaunin Kano ya ce shekararsa 40, kuma tun da ya taso masarautar Kano kawai ya sani yake kuma kauna.

''Shekarata 40, masarautar Kano kawai na sani kuma nake so, iyayena ma abin da suke fada kenan.

"Ni ba zan taba amincewa da karbar wadannan sababbin masarautun da aka kirkiro ba saboda ba sa cikin tarihinmu, kuma an kafa su ne kawai domin biyan bukatar wasu mutane.''

Wani mai lalurar ido wanda ke zaune a Kano, Saifullah Mukthar ya ce yana ganin wannan lamarin a matsayin abu mai kyau saboda zai inganta rayuwar mutane, ya kuma ba su damar iya shawarwari da sarakunan da ke kusa da su maimakon zuwa da nesa.

''Ina kallon kirkiro sababbin masauratun da aka yi a Kano a matsayin abu mai kyau, amma fa idan har 'yan siyasa ba su yi amfani da wannan matakin wajen biyan bukatunsu ba.

"Shugabanninmu dole su zauna su yi tunanin mutanen da ke karkashinsu a irin wadannan matsalolin, musamman ma iri na mai lalura, yin hakan zai sa duk mu mori wannan lamarin.''

Duk da cewa wani zaman kotu da aka yi a babbar Kotun Kano a ranar Juma'ar da ta gabata, kotun ta fitar da umarni na dakatar da kirkiro masarautun, amma gwamnan bai fasa tabbatar da sarakunan ba ta hanyar ba su takarda da sanduna a karshen makon da ya gabata.

Duk a cikin wadannan dai, Kano ba ita ce jiha ta farko a tarihi ba da ta taba fuskantar tirka-tirka tsakanin gwamanti da masarauta ba.

Jihar Imo

A shekara ta 2015, Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya ya taba samun irin wannan matsalar da tsohon Sarkin Owerri, marigayi Emmanuel Emenyonu Njemanze, wato mai sarautar OzuruIgbo V na Owerri a inda masarautar ta zargi gwamnan da raba kan jihar da kuma Owerri.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/ROCHAS
Image caption Gwamna Okorocha ya nemi takarar kujerar sanata a 2019 bayan da ya gama wa'adinsa na shekara takwas

A lokacin da lamarin ke faruwa tsakanin bangarorin biyu, an zargi gwamnatin Okorocha da dakatar da Eze Njemanze a matsayin mataimakin shugaban majalisar zartarwa ta Ndi-Eze.

Ya yi hakan ne saboda goyon bayan da masarautar ta bai wa Eze Cletus Ilomuanya wanda aka cire a matsayinsa na shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar.

Gwamnatin, a cikin wata sanarwa ta musanta dukkanin zarge-zargen a inda ta ce,''ba mu da hannu a dakatar da sarakuna hudu da aka yi da kuma karar fiye da mutum 50 da majalisar ta Eze ta kai.''

"Ta kuma kara da cewa ''...gwamnati ba za ta ki amsa umarni da kuma shawarwarin majalisar ba in dai za su taimaki jihar...''

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Eze Njemanze ya yi mulki na tsawon shekara 27 kafin ya rasa ransa a 2016 yana da shekara 84

Kamar yadda lamarin ya faru a Kano, gwamnatin Okorocha ta raba masarautar jihar zuwa al'ummomi guda biyar saboda ko wacce ta samu sarkinta.

A yau, jihar Imo tana da al'ummomi 637, kuma ko wacce tana da sarkinta, wadanda yawancinsu Gwamna Okorocha ne ya nada su.

JIHAR OYO

A kudu maso yammacin Najeriya, a jihar Oyo ma an taba fuskantar tirka-tirka tsakanin Oba Saliu Adetunji, Olubadan na Ibadan da Gwamna Abiola Ajimobi.

Hakkin mallakar hoto @AAAJIMOBI
Image caption Gwamna Ajimobi ya fadi a takarar da ya yi ta neman kujerar sanata a zaben 2019 bayan da ya yi shekara takwas yana mulkin jihar

A watan Augusta na 2017, Ajimobi ya kara wa wasu hakimai 21 matsayi zuwa sarakai wanda hakan ya sa suka zama sarakuna masu matsayi.

A karkashin sabon tsarin, Olubadan din wanda shi ne shugaba na gargajiya a Ibadan gaba daya, za a kira shi da 'Basarake mai matsayi', hakiman nasa da aka kara wa matsayi kuma za a kira su da 'Mai martaba'.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/SALIU ADETUNJI
Image caption Oba Adetunji shi ne Olubadan na 41 da aka nada a 2016 yana da shekara 88

Masu suka sun ce, da gwamnan ya kirkiro wadannan masarautun ya sauya tarihi wanda ya saba da Oba guda daya da kuma hakimai da dama wadanda za su iya ba da shawara a majalisar sarkin.

A wani bangaren kuma, gwamnan ya jaddada cewa ''ba tarihi muke sauyawa ba, kuma ba sauya al'ada muke ba, kuma ba za mu sauya al'adar yankin Ibadan ba; kawai muna kokarin kara daukaka masarautunmu ne.''

Olubadan din bai ji dadin abin da gwamnan ya yi ba a inda ya yi kokarin mayar da martani shi ma.

Wani kuma da bai goyi bayan matakin da Gwamna Ajimobi ya dauka ba shi ne tsohon gwamnan Oyo, Alhaji Rasheed Ladoja, wanda hakimi ne, an kara masa mukami zuwa sarki amma bai amshi mukamin ba a inda ya ce, ''... Ni ba zan iya zama sarki ba, ba tare da samun yankina ba.''

A watan Janairu na 2018, babbar kotun jihar Oyo ta dauki matakin gwamna Ajimobi a matsayin ''mara tushe da kuma hujja.''

Gwamnan ya daukaka wannan karar bisa hukuncin da aka zartar.

Labarai masu alaka