Na yi mkuka har ba hawaye a kurkuku - Zainab Aliyu
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Abin da ya faru da ni a gidan yarin Saudiyya – Zainab Aliyu

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Zainab Aliyu ta bayyana cewa ta sha kuka a kurkukun Saudiyya har sai da hawaye suka daina zubowa.

Ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi ta musamman da sashen Hausa na BBC.

Budurwar ta ba da labarin irin rayuwar da ta yi har tsawon wata hudu a gidan yarin Saudiyya, wajen da da wuya ka samu labarin yadda rayuwa take a cikinsa, musamman wadanda ake zargi da shigar da kwaya, saboda zai yi wahala mutum ya fito.

Zainab ta kuma bayyana yadda ta yi kewar 'yan uwanta musamman mahaifiyarta.

Labarai masu alaka