IS ta hallaka sojojin Nijar 29

Map

Kungiyar IS mai da'awar kafa daular musulunci ta yi ikirarin daukar alhakin mummunan harin da ya yi sanadin mutuwar a kalla sojojin Nijar 29 kusa da kan iyakar Mali.

A wata sanarwa da ta fitar ranar 16 ga watan Mayu, IS ta ce mayakanta sun far wa ayarin motocin sojojin Nijar a Tongo Tongo ranar 14 ga watan Mayu, sannan 40 daga cikin sojojin ne suka mutu ko suka jikkata.

Mayakan sun yi kwanton bauna ne a wani yanki inda aka taba kashe sojojin Amurka hudu a watan Oktoban 2017, yayin da suke wani atisaye na hadin gwiwa tsakanin dakarun Nijar da dakarun Amurka na musamman, inda a wancan lokacin ma mayakan IS suka far musu.

Kungiyar IS din ta dauki alhakin wannan harin.

Shi ma wannan harin na baya-bayan nan da aka kai ranar 13 ga watan Mayu, IS din ta ce mayakanta ne suka kai wa dakarun tsaron Nijar a gidan yarin Koutoukale kusa da Niamey, babban birnin kasar, inda ta ce ta kashe sojojin masu yawa.

Kafofin yada labarai sun ce, wasu mayaka dauke da manyan makamai ne suka kai hari gidan yarin mai cike da tsaro, har wani soja daya ya mutu.

Hukumomin Nijar dai sun ce sun dakile harin "ta'addancin."

Hakkin mallakar hoto EPA/US ARMY
Image caption Sojojin Nijar sun yi atisaye na Amurka a w farkon wannan shekarar

Ana ganin dai IS na zafafa kai hare-hare a yankin Afrika ta Yamma a wannan shekarar, musamman a Najeriya da makwabtanta kamar Nijar.

Haka ma mayakan kungiyar al-Qaeda na kara yin karfi a yankin.

Sun fi karfi a Mali, inda aka tura dakarun Faransa tun shekarar 2013 don kare kasar daga mayakan na al-Qaeda daga yin tasiri a babban birnin kasar, sai dai duk da haka su kan kai hare-hare kan iyakoki.

A ranar Alhamis ne aka gano gawarwakin wasu sojojin Nijar din 11 da ba a gansu ba tun ranar Talata, al'amarin da ya sa yawan wadanda aka kashe ya karu zuwa 28.

Yaya harin ya faru?

Sojojin suna neman mayakan ne wadanda suka kai hari gidan yarin da ke cike da tsaro wanda ke wajen birnin Niamey a ranar Talata, kamar yadda wani mai magana da yawun gwamnati ya shaida wa BBC.

Mista Zakariyyah ya bayyana wa BBC cewa ''daya daga cikin motocin sojojin ta fada cikin nakiya inda mayakan suka fara harbin sojojinmu.''

A baya dai an bayyana cewa sojoji 17 ne aka kashe a kwanton baunar da aka yi.

Mista Zakariyyah bai bayyana wadanda suka kai harin ba amma ya bayyana cewa lamarin ya faru ne kusa da inda aka kashe dakarun Amurka da kuma na Nijar biyar shekaru biyu da suka wuce.

Nijar na daya daga cikin kasashe biyar da suka yi hadakar runduna ta musamman domin yaki da 'yan tayar da kayar baya a yankin Sahel.

Kasashen sun hada da Burkina Faso da Chadi da Mali da kuma Mauritaniya.

Kungiyar hadakar dakarun wacce ake yi wa lakabi da G-5 Sahel na da goyon bayan karfafan sojoji na Faransa 3,000.

Kai hare-hare ga sojojin kawance na Faransa

Sharhi daga Louise Dewast, wakilin BBC na yammacin Afirka

Wannan shi ne hari mafi muni da aka taba kai wa a yammacin Nijar, inda yanki ne da dakarun gwamnati da kuma sojojin kawance ke yaki da kungiyoyin al-Qaeda da kuma IS.

Hukumomi sun bayyana cewa wannan hari ne mai dauke da abubuwa da dama inda har 'yan tayar da kayar bayan suka yi amfani da bama-bamai.

Duk da shekarun da aka dauka ana kawo dakaru daga Faransa da Amurka da kuma na Majalisar Dinkin Duniya, yankin na nan a gidan jiya.

Kungiyar da ake wa lakabi da ''Islamic State'' a yankin Sahara, a 'yan kwanakin nan sun sha fafatawa da kuma kokarin dakile hare-haren da dakarun gwamnati ke kai masu wanda hakan ya zama matsala ga kokarin kawar da su.

Wani masanin tsaro kuma mai bincike a yankin wato Héni Nsaibia, ya bayyana cewa a ganinsa daya daga cikin dalilan da ya sa 'yan tayar da kayar bayan suka samu irin wannan galabar har da yadda sojojin Faransa suka fi mayar da hankali kan tsakiyar Mali da kuma ayyukan da suke gudanarwa a 'yan kwanakin nan a Burkina Faso.

Ya kuma bayyana cewa watakila kuma 'yan tayar da kayar bayan na amfani da wata huduba da Shugaban Kungiyar IS wato Abu Bakr al-Baghdadi ya yi a wani faifai na bidiyo inda ya bukaci 'yan kungiyar su ci gaba da zafafa hare-harensu.

Labarai masu alaka