Allah ya ba ni coma banda mata ta gari- Adam Zango
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Adam A Zango: 'Abin da ya sa nake auri saki'

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

Shahararren dan wasan Hausa nan, Adam A Zango ya shaida wa BBC dalilin da ya sa yake yawan auran mata kuma daga bisani ya sake su.

Dan wasan ya ce ba kasa zama yake yi da mace ba, "ba zan iya fada muku abin da ya hada shi da matata ta farko, da matata ta biyu da kuma matata ta uku ba."

Ya kuma ce: "Allah Ubangiji ya rubuta wa mutum abin da zai faru da shi tun daga farkon haihuwarsa har zuwa ranar mutuwarsa."

Daga nan, Zango ya danganta batun da kaddara daga Ubangiji inda ya ce: "Allah Ya ba ni komai da na roke shi, amma ban da mace."

Rayuwar Adam A Zano a takaice

Hakkin mallakar hoto Adam Zango
  • An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
  • Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
  • Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi karatun Firamare
  • Talauci ya hana shi ci gaba da karatu a wancan lokacin
  • Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher - mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake rawa
  • Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade da raye-raye
  • Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya shi da kansa
  • Ya fito a fim fiye da 100 a tsawon shekara 16.

Labarai masu alaka